Wutar Lantarki: Ƴan Najeriya Sun Sake Shiga Matsala Karo na 2 cikin Awanni 24

Wutar Lantarki: Ƴan Najeriya Sun Sake Shiga Matsala Karo na 2 cikin Awanni 24

  • Babban layin wutar lantarki a Najeriya ya sake katsewa ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, 2024 karo na biyu cikin sa'o'i 24
  • Kamfanin raba wuta na Eko ya ce layin wutar ya lalace da misalin ƙarfe 9:17 na safiya amma ma'aikata na kokarin gyarawa
  • Wannan dai na zuwa ne bayan ɗauke wuta a jiya Litinin da daddare sakamakon lalacewar babban layin wuta na ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wutar lantarki ta sake katsewa a Najeriya sakamakon lalacewar babban layin wutar na ƙasa karo na biyu cikin sa'o'i 24.

Babban layin da ke samar da wutar lantarkin ya kuma katsewa da misalin ƙarfe 9:17 na safiyar yau Talata, lamarin da ya jawo matsala.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya zabtare 55% a farashin shinkafa da wasu kayan abinci

Layin wutar lantarki.
Wutar lantarki ta ƙara lalacewa karo na 2 cikin awanni 24 a Najeriya Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Kamfanin da ke da alhakin rarraba wutar lantarki na Eko watau EKEDC ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wutar lantarki ta katse a Najeriya

"Muna sanar da abokan huldarmu masu daraja cewa layin wutar lantarki na ƙasa ya katse da misalin karfe 9:17 na safe wanda ya jawo ɗaukewar wuta.
"A halin yanzu mun duƙufa domin maido da wutar lantarki, za mu sanar da ku halin da ake ciki da zarar komai ya daidaita," inji sanarwar.

Wannan shi ne karo na biyu da layin wutar ya katse cikin awanni 24 bayan wanda ya faru a daren jiya Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024.

Yadda ake fama da rashin wuta a Najeriya

A binciken da aka yi a shafin yanar gizo na ISO da kamfanin raba wuta TCN ya nuna babu ko da megawatta guda da karfe 7:00 na daren ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dauki mataki bayan matashi ya cinnawa kakarsa wuta a Jigawa

Ma'ana babu wutar da aka tura daga tashar samar da wutar lantarki zuwa kamfanoni 11 na rarraba wuta a Najeriya.

Gwamnati za ta inganta wutar lantarki

Ku na da labarin gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ana wasu manyan ayyuka da za su inganta wutar lantarki a Najeriya.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka, inda ya ce shirin zai kawo karuwar hasken lantarki a faɗin ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262