Karshensu Turji Ya Zo: Najeriya za Ta Shigo da Jiragen Yaki Sama da 30

Karshensu Turji Ya Zo: Najeriya za Ta Shigo da Jiragen Yaki Sama da 30

  • Gwamnatin tarayya na shirin shigo da jiragen yaki domin murƙushe masu ta'addanci a Najeriya musamman yan bindiga
  • Shugaban sojojin saman Najeriya, Hassan Abubakar ne ya jagoranci tawagar masana domin cinikin jiragen a kasar Italiya
  • Ana sa ran cewa zuwan jiragen zai taimaka wajen kakkaɓe yan bindiga da sauran miyagu da suka fitini al'ummar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar sojin saman Najeriya ta fitar da sanarwa kan shirin sayo jiragen yaki daga Turai.

Tawagar masana karkashin jagorancin shugaban sojojin ruwan Najeriya, Hassan Abubakar ne ke jagorantar cinikin jiragen.

Jirgin yaki
Najeriya ta saye jiragen yaki 34. Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da rundunar sojin saman Nigeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

'Babu dawowa bariki sai an gama da yan bindiga baki daya,' An yi wa sojojin Najeriya caji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a sayo jiragen yaki a Najeriya

Rundunar sojin saman Nigeriya ta bayyana cewa yanzu haka tana cinikin jiragen yaki ƙirar M-346 FGA guda 24.

Haka zalika rundunar ta bayyana cewa cikin kayan yakin da take saye akwai jirage guda goma kirar AW-109 daga kasar Italiya.

Yaushe jiragen za su iso Najeriya?

Daraktan yada labaran NAF, Olusola Akinboyewa ya ce a yanzu haka jirage kirar AW-109 guda biyu sun iso Najeriya sannan zuwa ƙarshen 2026 za a gama samun sauran guda goman.

Olusola Akinboyewa ya ce jirage kirar M-346 guda 24 za su iso Najeriya ne zuwa karshen shekarar 2025 mai zuwa.

Tawagar da ta tafi sayo jiragen yaki

Rahotanni sun nuna cewa cikin tawagar da tafi sayo jiragen akwai shugaban sojojin saman Najeriya, Hassan Abubakar.

Daily Trust ta wallafa cewa akwai wakilai daga ma'aikatar tsaron Najeriya da ma'aikatar harkokin kuɗi ta kasa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya sake dagulewa, an nada sabon shugaban jam'iyyar, bayanai sun fito

An ba sojoji umarni kan yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi kira na musamman ga sojoji kan tunkarar yan bindiga da sauran miyagu.

Manjo Janar Kelvin Aligbe ne ya sake yi wa sojojin caji a wani taron jarrabawar karin matsayi da aka yi wa sojojin Najeriya a jihar Ondo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng