Jiragen Yaki 'Super Tucano' Guda 6 Sun Baro Amurka, Zasu Iso Najeriya Ba da Jimawa Ba, NAF
- Rundunar sojin sama NAF ta tabbatar da cewa jiragen yaƙin super tucano guda shida sun baro Amurka
- A wani jawabi da kakakin NAF ya fitar, yace jiragen zasu biyo ta wasu ƙasashe biyar kafin isowar su
- Yace an gama shirye-shirye ƙaddamar da su da zaran sun iso Najeriya, za'a sanar da haka nan gaba
Kashin farko na jiragen yaƙin 'A-29 Super Tucano' sun baro haɗaɗɗiyar ƙasar Amurka, suna kan hanyarsu ta zuwa Najeriya.
KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: NAFDAC Ta Amince da Sabbin Rigakafin COVID19, Ta Faɗi Amfani da Hatsarinsu
Kakakin rundunar dakarun sojin sama, NAF, Edward Gabkwet, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis a shafn sada zumunta na facebook.
yace jiragen sun baro ƙasar Amurka ranar Laraba, kuma ana tsammanin isowar su Najeriya a kowane lokaci.
Yace: "Kashin farko na Jiragen yakin super tukano guda 6 sun baro Amurka jiya Laraba 14 ga watan Yuli, suna kan hanyar zuwa Najeriya."
"Jiragen shida zasu keto ƙasashen biyar da suka haɗa da, Canada, Greenland, Iceland, Spain da Algeria kafin su iso Najeriya a ƙarshen watan Yuli 2021."
"An shirya bikin ƙaddamar da jiragen zuwa cikin kayan aikin rundunar sojin sama a hukumance jim kaɗan bayan isowarsu a watan Agusta 2021, kuma za'a sanar a lokacin da ya dace."
Gwamnatin tarayya ta siyo jirage 12
A watan Fabrairun da ya gabata ne, gwamnatin tarayya ta siyo jiragen 'Super Tucano' guda 12 akan kuɗi $496 miliyan.
A baya, an sha sanar da ranakun isowar kashin farko na jiragen, kafin wannan sanarwar ta yau Alhamis.
Gwamnati na fatan jiragen zasu taimakawa sojoji a yaƙin da suke yi da yan ta'adda a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Bayan Cece-Kuce, Sanatoci Sun Amince da Naɗin Wani Kwamishinan Zaɓe, INEC
Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin yan Najeriya dangane da wannan labarin.
Dondo Dagba, yace:
"Wai meyasa ba zaku iya boye irin wannan cigaban bane, kubar waɗannan yan ta'adda da yan bindigan cikin duhu? wannan na nuni da cewa kuna kasuwancin ku ne ba wani abu ba."
Gift-tony Nwaozuzu, yace:
"Ina mamakin meyasa muke bayyana komai a ƙasar nan har da waɗanda bai kamata ba. Ina da tambaya, shin haka ƙasar Amurka suke yi idan sun sayi abu ga sojojin su? gaskiya ya kamata mu gane."
A wani labarin kuma EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya
Hukumar EFCC ta ƙaddamar da sabuwar manhajar bankaɗo bayanan masu aikata cin hanci a Najeriya.
Shugaban hukumar ya bayyana yadda yan Najeriya zasu tura bayanai da hotunan masu aikata laifin.
Asali: Legit.ng