'Ba Yan Ta'adda ba ne', Sarkin Zazzau Ya Fadi Yadda Fulani Suke, Ya Kawo Dalili

'Ba Yan Ta'adda ba ne', Sarkin Zazzau Ya Fadi Yadda Fulani Suke, Ya Kawo Dalili

  • Yayin da ake cigaba da zargin wasu Fulani da hannu a ayyukan ta'addanci, Sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli ya yi tsokaci
  • Basaraken ya bayyana yadda aka san Fulani tun a baya inda ya ce babu abin da ya haɗa su da ta'addanci ta kowane fuska
  • Sarkin ya bayyana yadda yake alfahari da kasancewarsa Fulani inda ya ce duk danginsa daga sama har kasa jininsu ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Sarkin Zazzau, Mai Martaba Nuhu Bamalli ya yi magana kan ta'addanci da ke faruwa musamman a Arewacin Najeriya.

Basaraken ya ce ta'addanci ba halin Fulani ba ne saboda ba haka dabi'unsu suke ba tun farko da aka sani.

Kara karanta wannan

Neman beli: Kotu ta kara hankaɗa keyar jami'in Binance zuwa kurkuku

Sarkin Zazzau ya yi magana kan halayen Fulani
Sarkin Zazzau, Mai Martaba, Nuhu Bamalli ya koka kan halayen wasu Fulani a yanzu. Hoto: Kasar Zazzau a jiya da yau.
Asali: Facebook

Sarkin Zazzau ya fadi asalin halayen Fulani

Sarkin ya bayyana haka a jiya Asabar 12 ga watan Oktoban 2024 a taron kungiyar Fulani, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Martaba Bamalli ya ce asali yadda aka san Fulani shi ne suna rike sanda da adda yayin kiyo a daji a kowane lokaci.

Martanin basaraken na zuwa ne yayin da ake zargin Fulani a harkar ta'addanci da ya jefa al'umma cikin mummunan yanayi.

Sarkin Zazzau yana alfahari da Fulani

"Ina matukar alfahari da kasancewata Fulani, iyaye da kakanni na duka Fulani ne."
"Babu wani dalili da zai saka ba zan yi alfahari da yare na da al'adu ba, kowace ƙabila ana samun gura-gurbi."
"Ya kamata Fulani sun kare martabarsu, bai kamata Bafulatani ya dauki AK-47 ba, abin da ya kamata shi ne ya dauki sanda ko adda domin yankawa dabbobi ciyawa."

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya fadi abin da zai faru ga masu ba yan ta'adda bayanai

- Nuhu Bamalli

Yan ta'adda sun shiga uku a Arewa

Kun ji cewa Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya umurci babban hafsan tsaro na kasa da sauran hafsoshin tsaro da su koma jihar Sokoto.

An ce ministan ya dauki wannan matakin ne da nufin ƙara tsananta ayyukan soji a jihar domin kawar da barazanar da ‘yan bindiga ke yi.

Umarnin ya jaddada kudirin gwamnati na maido da zaman lafiya da tsaro a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, da Kebbi da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.