'Ban Yi Nadama ba', Malamin Musulunci kan Zaben Musulmi da Musulmi, Ya Fadi Dalili

'Ban Yi Nadama ba', Malamin Musulunci kan Zaben Musulmi da Musulmi, Ya Fadi Dalili

  • Malam Salihu Abubakar Zaria ya bayyana cewa ko kadan bai yi nadamar zaben Bola Tinubu a tsarin Musulmi da Musulmi ba
  • Sheikh Salihu ya ce ko kadan ba tsarin Musulmi da Musulmi ba ne ya kawo damuwar da ake ciki inda ya ce daga Allah ne
  • Hakan na zuwa ne yayin da yan Najeriya da dama ke kokawa kan mulkin Bola Tinubu da suke zargin malamai da jawo musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Sheikh Abubakar Salihu Zaria ya yi magana kan zaben Musulmi da Musulmi a Najeriya.

Shehin malamin ya ce har zuwa yanzu bai yi nadamar zaben Musulmi da Musulmi ba a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fadi lokacin fita a kangi, ya kawo hanyoyin magance matsaloli

Malamin Musulunci ya ce ko gobe zai sake zaben Musulmi da Musulmi
Sheikh Abubakar Salihu Zaria ya ce bai yi nadamar zaben Musulmi da Musulmi ba. Hoto: Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria.
Asali: Facebook

Sheikh Salihu Zaria ya magantu kan Muslim/Muslim

Malamin ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da DCL Hausa da aka wallafa a yau Lahadi 13 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Salihu ya ce duk da shawarar da suka bayar kan Musulmi da Musulmi amma sun fito sun fadawa shugabanni gaskiya.

Shehin malamin ya ce a matsayinsa na cikakken Bahaushe har da Yarbanci sai da ya yi magana domin isar da sako ga Bola Tinubu.

'Ban yi nadamar zaben Muslim/Muslim ba' - Salihu Zaria

"Ni a matsayina na Musulmi, ko yau Musulmi da Musulmi suka fito takara su zan sake zabe."
"Ban taba nadamar shawarar da na bayar na zaben Musulmi da Musulmi ba, ban taba ba."
"Ni dan nan jihar Kaduna ne na san abubuwa da suka faru a baya, Annabi ya ce ba a saran mumini a rami daya."

Kara karanta wannan

'Ba daidai ba ne': Malamin Musulunci ya sha suka kan magana game da karin kudin mai

"Matsala ce Allah ya kawo ta karkashin wannan siyasa da ake ciki amma ba tsarin Musulmi da Musulmi ne ya kawo ta ba."

- Sheikh Salihu Abubakar Zaria

Sheikh Salihu Zaria zai kara aure

Kun ji cewa Shehin malamin addinin Musulunci, Alkali Abubakar Salihu Zariya ya ce maganar ƙara aure da zai yi na nan daram dam.

Alkali Abubakar Zariya ya ce soyayya da yabon da ya ke yi wa matarsa Hajiya Jamila ba shi zai hana ya auri sahibarsa Sumayya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.