'A Fita Zanga Zanga,’ Yadda Aka yi Rubdugu ga Tinubu kan Tashin Kudin Fetur

'A Fita Zanga Zanga,’ Yadda Aka yi Rubdugu ga Tinubu kan Tashin Kudin Fetur

  • A ranar Laraba da ta wuce ne kamfanin NNPCL ya yi karin kudin man fetur ana tsaka da wahalar rayuwa a kasar nan
  • Lamarin ya tada kura musamman tsakanin masu karamin karfi kasancewar suna fama da abin da za su saka a bakin salati
  • Manyan yan siyasa da kungiyoyi sun soki Bola Ahmed Tinubu bisa karin kudi, wasu suka ce NNPCL ya karya doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Karin kudin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi na cigaba da jan hankulan al'umma a fadin Najeriya.

A ranar Laraba ne aka samu karin kudin man fetur inda litar mai ta haura N1,000 a mafi yawan gidajen man gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi albishir ga yan kasa kan saukar farashin fetur

Bola Tinubu
An dura kan Tinubu a kan karin kudin fetur. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Kola Sulaimon
Asali: UGC

Vanguard ta haɗa rahoto kan yadda wasu daga cikin kungiyoyi da yan siyasa suka yi raddi ga gwamnatin Bola Tinubu kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuɗin fetur: Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu

1. Maganar Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi na kara jefa al'umma a wahala.

Atiku ya wallafa a Facebook cewa babban abin haushi shi ne shugaban kasa bai damu da wahalar da ake ciki ba.

2. Amaechi ya kawo maganar fita zanga zanga

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi ya yi kira ga matasan Najeriya da su fito zanga zanga kan ƙarin kudin mai.

Legit ta ruwaito cewa Rotimi Amaechi ya ce abin mamaki yadda yan Najeriya suka ki fitowa zanga zangar kan karin kudin mai da aka yi.

Kara karanta wannan

Ana wayyo da karin farashin fetur da NNPCL ya yi, IPMAN za ta ballo ruwa

3. Jam'iyyar PDP ta dura kan Tinubu

Haka zalika jam'iyyar PDP ta yi zazzafan martani ga shugaba Bola Tinubu kan karin kudin man fetur a Najeriya.

PDP ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta canja tsare tsaren da suka jefa al'umma cikin wahalar rayuwa.

4. NACCIMA ta ce Tinubu zai rusa sana'o'i

Shugaban kungiyar NACCIMA, Dele Oye ya ce karin kudin mai zai jefa al'umma da sana'o'i cikin matsala.

Dele Oye ya ce matuƙar aka tafi a haka to sana'o'i da dama za su durƙushe kuma mutane za su tagayyara.

5. Yan kwadago sun bukaci rage kudin fetur

Kungiyoyin kwadago na TUC da NLC sun bukaci gwamnatin tarayya ta rage kudin mai bayan karin da aka yi a ranar Laraba.

Yan kwadago sun ce lamarin zai kara jefa ma'aikata cikin damuwa saboda zai kara kawo tsadar rayuwa.

Inda ake samun man fetur da araha

A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Laraba aka wayi gari a Najeriya da karin kudin fetur wanda lamarin ya tayar da kura a tsakanin al'umma.

Kara karanta wannan

"Ba laifin mijina ba ne": Uwargidan Tinubu ta fadi lokacin da talaka zai samu sauki

An samu wasu gidajen mai mallakar yan kasuwa da suke sayar da fetur a kasa da farashin kamfanin NNPCL a birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng