Zo Ka Nema: Rundunar Sojan Sama Ta Fara Daukar Sababbin Sojoji, Ta Kafa Sharudda

Zo Ka Nema: Rundunar Sojan Sama Ta Fara Daukar Sababbin Sojoji, Ta Kafa Sharudda

  • Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) na gayyatar wadanda suka kammala karatun digiri da su zo su nemi aikin soja a bangaren DSSC
  • Za a fara rajistar cike fom din neman aikin sojan saman a ranar Litinin, 14 ga Oktoba, kuma za a rufe ranar Talata, 26 ga Nuwamba, kuma kyauta ne
  • Sanarwar da rundunar ta fitar ta ƙunshi matakan neman aikin, abubuwan da ake bukata, da kuma wadanda suka cancanci neman aikin sojan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Rundunar Sojan Sama ta Najeriya (NAF) ta sanar da fara daukar sababbin sojoji a bangaren Direct Short Service Cadets (DSSC).

Rundunar sojin saman ta ce ta ce masu sha'awa kuma wadanda suka cancanta za su yi rajista ne a shafinta na www.nafrecruitment.airforce.mil.ng.

Kara karanta wannan

Atiku ko Wike? Shugabanni sun bayyana wanda ya haddasa rikicin da ya mamaye PDP

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta sanar da daukar ma'aikata na DSSC.
Za a fara rajistar neman aikin sojan sama ta yanar gizo a ranar Litinin, 14 ga Oktoba. Hoto: @NigAirForce
Asali: Twitter

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X, za a fara rajistar ne a ranar Litinin, 14 ga Oktoba, sannan za a rufe ranar 26 ga Nuwamba, kuma kyauta ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda suka cancanci neman aikin

Dole ne wadanda za su nemi aikin sojan saman Najeriya su kasance:

  • Haifaffun 'yan Najeriya ne.
  • Masu tsayin 1.66m ga maza da kuma tsayin 1.63m ga mata.
  • Masu cikakkiyar lafiya bisa binciken likita
  • Kotu ba ta taba samunsu da aikata wani laifin ta'addanci ba.
  • Masu shekaru 20 zuwa 30 (wadanda aka haifa kafin 27 ga Satumbar 1995 ba za su iya nema ba) in banda wadannan:

a. Likitoci masu ba da shawarwari su kasance tsakanin shekaru 25 zuwa 40 (ban da wadanda aka haifa kafin 27 Satumba 1985.)

b. Jami'an sojin da suka haura shekaru 30 (wadanda aka haifa kafin 27 ga watan 1995) ba za su nemi aikin ba.

Kara karanta wannan

'Yar kasar Canada ta shiga matsala a Najeriya, NDLEA ta cafke kwayoyin N9bn

DSSC: Abubuwan da mutum ke bukata

  • Dole ne masu sha'awar neman aikin su mallaki mafi ƙaranci 'Second Class Upper Division' ga masu digiri na daya da kuma Upper Credit ga masu HND.
  • Bugu da kari, dole mutum ya kasance yana da kiredit a Ingilishi da Lissafi da kuma wasu darusa uku. Masu ilimin sarrafa na'ura mai kwakwalwa na da tagomashi.
  • Dole masu son shiga aikin sojan saman bangaren DSSC su mallaki shaidar kammala NYSC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.