"Ba Laifin Mijina ba ne": Uwargidan Tinubu Ta Fadi Lokacin da Talaka Zai Samu Sauki

"Ba Laifin Mijina ba ne": Uwargidan Tinubu Ta Fadi Lokacin da Talaka Zai Samu Sauki

  • Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta ce ba mijinta, shugaba Bola Tinubu ne ya jefa Najeriya a tsadar rayuwar da ake ciki ba
  • Sanata Oluremi Tinubu ta ce duk da cewa an janye tallafin fetur, wanda ya sa litar ta koma N1,030 daga N198, bai kamata a ga laifin mijinta ba
  • Matar shugaban kasar ta ba 'yan Najeriya tabbacin cewa nan da shekaru biyu masu zuwa Najeriya za ta samu gagarumin ci gaba mai dorewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - Sanata Oluremi Tinubu ta ce bai kamata a dorawa mijinta, Shugaba Bola Tinubu laifi kan halin matsin tattalin arziki da Najeriya ke ciki a yanzu ba.

Kara karanta wannan

Farashin fetur: Ministar Tinubu ta yi albishir mai daɗi ga yan Najeriya

'Yan Najeriya sun fara shiga kuncin rayuwa bayan da Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin fetur wanda hakan ya sa litar fetur ta kai N1,030 daga N198 a yau.

Uwargidan shugaban kasa Tinubu ta yi magana kan tsadar rayuwa
Uwargidan Tinubu ta ce ba mijinta ne ya jawo tsadar rayuwa a Najeriya ba. Hoto: @SenRemiTinubu
Asali: Twitter

Uwargidan Tinubu ta kare gwamnatinsu

A ziyarar da ta kai fadar Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi a ranar Alhamis, Sanata Oluremi ta ce har yanzu rarrafe gwamnatin Tinubu ke yi, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uwargidan shugaban kasar ta je Ife ne domin kaddamar da wani otal da kuma titi mai nisan kilomita 2.7 da Sarkin Ife ya ba da kyauta ga jami'ar Ọbafẹmi Awolọwọ da ke Ile Ife.

Sanata Oluremi ta ce:

“Shekaru biyu ne kacal da fara mulkinmu, ba mu ne musabbabin halin da ake ciki ba, muna kokarin gyara barnar da aka yi da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma.

Kara karanta wannan

“An samu tsaro a Najeriya”: Ribadu ya fadi bambancin gwamnatin Tinubu da Buhari

"Mun san cewa an cire tallafin man fetur, amma da ikon Ubangiji Najeriya za ta samu ci gaba mai yawa daga nan zuwa shekaru biyu masu yawa."

"Mijina ba shi da hadama" - Oluremi Tinubu

Uwargidan shugaban kasar ta kara da cewa mijinta ba mai hadama ba ne, tana mai godewa Allah da ya sa ya zama shugaban kasar Najeriya.

“Muna godiya ga Allah da matsayin da muka samu, ni da mijina, ba mu da hadama amma muna gode wa Allah da abin da Ya yi mana.
"Ba kasafai masu kudi ke samun irin wannan matsayin ba, ba za mu ba Najeriya kunya ba, kuma da taimakon Ubangiji za mu kai kasar nan tudun mun tsira."

- Remi Tinubu

Uwargidan Tinubu ta kai dauki Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa uwargidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta kai ziyarar jaje a Maiduguri domin nuna alhini kan ambaliyar ruwan da ta auku.

Kara karanta wannan

Kungiya ta fadawa Tinubu ribar da zai samu idan ya sasanta rikicin masarautar Kano

Oluremi Tinubu da ta samu wakilcin matar mataimakin shugaban ƙasa, ta ba da gudunmawar N500m domin tallafawa mutanen da lamarin ya shafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.