Masu Zuba Jari a Kasar Koriya Za Su Gina Matatun Mai a Najeriya, Bayanai Sun Fito
- Karamin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya bayyana cewa Najeriya ta jawo wasu masu zuba jari daga Koriya ta Kudu
- Ministan ya ce gamayyar masu zuba jarin sun nuna sha'awarsu ta gina matatun mai hudu a wurare daban daban na kasar nan
- Heineken Lokpobiri ya ce tuni gwamnati ta aikawa masu zuba jarin katin gayya tare da alwashin ba masu zuba jari damar kasuwanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce wata gamayyar masu zuba jari daga Koriya ta Kudu ta kammala shirin gina matatun mai hudu a wurare daban-daban a Najeriya.
Karamin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ne ya bayyana haka a wajen wani taro da kungiyar masu matatun mai ta Najeriya ta shirya a Legas.
Najeriya ta jawo masu zuba jari
A cewar Lokpobiri, gwamnatin tarayya na karfafa gwiwar masu zuba jari da su gina matatun man ta hanyar samar da muhallin yin hakan ga kowa, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya ce kwanan nan aka amince da gayyatar gamayyar masu zuba jarin domin tattauna yadda lamarin zai kasance amma bai bayyana sunayensu ba.
"Muna karfafa masu zuba jari da su gina matatun mai ta hanyar samar da fage da kuma yanayi mai kyau a gare su."
- A cewar ministan.
'Yan Koriya ta Kudu za su gina matatu
Heineken Lokpobiri ya bayyana cewa gamayyar masu zuba jari daga Koriya ta Kudu za su gina matatun mai hudu da kowacce za ta iya tace ganga 100,000 na mai a rana.
"A baya-bayan nan aka tura goron gayyata ga wata gamayyar masu saka hannun jari daga Koriya ta Kudu, wadda ke da niyyar gina matatun mai hudu a wurare daban-daban a Najeriya.
"Mun yi amfani da tsarin haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin saka jari a harkar man fetur din kasar da kuma samar da karin matatun mai."
- A cewar Lokpobiri.
IPMAN ta kalubalanci kamfanin NNPC
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar IPMAN ta ce har yanzu 'yan kasuwa ba su fara sayen mai kai tsaye daga matatar man Dangote ba, sabanin matsayar da NNPC ya dauka.
IPMAN ta ce NNPC ba ta janye daga zama 'yar tsakiya tsakanin Dangote da 'yan kasuwa ba, duk da shaidawa duniya cewa ta daina tsoma baki a alakar matatar da 'yan kasuwar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng