Kungiyar ‘yan kasuwan man fetur na Najeriya sun shirya gina matatun mai na dala biliyan $3bn

Kungiyar ‘yan kasuwan man fetur na Najeriya sun shirya gina matatun mai na dala biliyan $3bn

- Kungiyar IPMAN sun shirya gina matatun mai a jihohi guda biyu a Najeriya

- Kungiyar IPMAN ta ce tana son ta gina matatun man da za su rika tace gangunan danyen man fetur guda 200,000 a kowani rana

Kungiyar ‘yan kasuwan man fetur na Najeriya (IPMAN) sun shirya gina matatun mai na dala biliyan $3bn wanda yayi dadai da naira triliyan(N1.08t) a jihohi guda biyu a Najeriya.

Shugaban kungyar IPAN, Mr Chinedu Okoronkwo, ya bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labarun News Agency of Nigeria (NAN) a ranar Laraba.

A watan Yuni na shekara 2014 Kungiyar IPMAN ta saya filaye masu girman hecta 1,000 a jihar Kogi da Bayelsa dan gina matatun man da za su rika ta ce gangunan danyen mai 200,000 a kowani rana.

Kungiyar ‘yan kasuwan man fetur na Najeriya sun shirya gina matatun mai na dala biliyan $3bn
Kungiyar ‘yan kasuwan man fetur na Najeriya sun shirya gina matatun mai na dala biliyan $3bn

Okoronkwo ya ce an jinkirta aikin gina matatun man da ya kamata su fara shi tun a shekaru biyu da suka wuce saboda rikicin shugabancin da ya barke a cikin kungiyar, amma yanzu da aka shawo kan matsalar za su fara aikin.

KU KARANTA : Babu yadda za a iya kari a cikin kasafin kudin shekara 2018 – Daraektan ofishin hukumar kasafin kudi

Shugaban kungiyar IPMAN ya ce jagororin kungiyar su fara tattauna da masu zuba hannun jari da abokan huldar su akan yadda za su fara aikin.

“Aikin gina matatun mai na dala biliyan $3bn zai fara ne yayin da muke tattaunawa da masu zuba hannun jari da abokan hulda mu," inji Okonkwo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng