Gwamnatin Buhari zata sake gina sabbin matatun man fetur 2 a Najeriya
- Buhari zai sake gina matatun man fetur 2 a Najeriya
- Za'a gina su ne a kudu
- Ana sa ran Najeriya ta dena shigowa da tattacen mai daga waje
Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce ta shirya tsaf domin kara gina wasu matatun mai na musamman har guda biyu a jahohin Imo da Delta dukkan su dake a kudancin Najeriya.
KU KARANTA: Ranar da Kwankwaso ya bar APC ban yi bacci ba - Ganduje
Kamar yadda muka samu, kamfanin albarkatun man fetur na Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) shi ne ya sanar da hakan inda kuma ya kara da cewa matatun man za su rika tace akalla gangar danyen mai dubu 200 a kullum idan aka kammala su.
Legit.ng ta samu cewa babban Manajan Daraktan hukumar ta kamfanin na Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) Dakta Mai Kanti Baru shine ya sanar da hakan ga manema labarai yayin kaddamar da shirin fara lalubo hanyar gina matatun man.
Da wannan matakan da ma sauran da ake kan yi na gwamnatin tarayya dai ana ganin nan gaba kasar ta Najeriya za ta dena shigo da tattacen danyen mai daga kasar waje.
A wani labarin kuma, Sakataren kungunyar kwadago a Najeriya watau Nigeria Labour Congress (NLC) a turance mai suna Peter Ozo-Esan ya baiwa daukacin ma'aikatan Najeriya tabbacin cewa kafin shekarar 2018 gwamnatin tarayya zatayi karin albashi.
Mista Ozo-Esan ya bayar da wannan tabbacin ne a garin Abuja ranar Talatar da ta gabata lokacin da yake zantawa da kamfanin dillacin labarai inda ya ce tuni shire-shire sun yi nisa akan lamarin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng