NAHCON: Ana Fargabar Kudin Aikin Hajji Zai Koma N10m a Najeriya, An Gano Dalili

NAHCON: Ana Fargabar Kudin Aikin Hajji Zai Koma N10m a Najeriya, An Gano Dalili

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta iya ci gaba da ba mahajjatan Najeriya (Musulmi) tallafi yayin biyan kudin zuwa aikin Hajji ba
  • Gwamnatin ta bakin hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta bayyana janye tallafin ne a cikin wata sanarwa da Fatima Sanda Usara ta fitar
  • A yanzu da gwamnati ta janye tallafin, ana fargabar mahajjatan 2025 za su biya kusan N10m yayin da ake canja Naira kan dala a kan N1,650/$1

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta tallafa wa alhazai ba a shekarar 2025.

An bayyana cewa galibi tallafin da gwamnati ke bayar wa na zuwa ne a matsayin rangwame ga maniyyata wajen samun dala a farashi mai sauki daga CBN.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Uba Sani ta ciyo bashin N36bn a Kaduna? An gano gaskiya

Gwamnatin tarayya ta janyewa alhazan Najeriya tallafin zuwa aikin Hajji
NAHCON: Gwamnati ta janye tallafin aikin Hajji, ana fargabar maniyyata za su biya N10m. Hoto: @HaramainInfo
Asali: Twitter

NAHCON ta janyewa alhazai tallafi

Bayanin janye tallafin da gwamnati ta yi na kunshe ne a cikin wata sanarwar daga mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Fatima Sanda ta ce:

"Gwamnati ba za ta iya ci gaba da ba da rangwame na kudin aikin Hajji ga maniyyata ba, walau a karkashin ma'aikatan zuwa Hajji na masu zaman kansu ko kuma na gwamnati."

Hakan na nufin idan har aka ci gaba da canja Naira akan N1,650/$1, kowane mahajjaci zai biya kusan N10m na kudin aikin hajji yayin da maniyyata za su biya akalla $6,000.

Jihohi sun fara karbar kudin Hajjin 2025

Yayin da NAHCON ta kasa ba ta kai ga bayyana kudin aikin hajjin shekarar 2025 ba, hukumar jin dadin alhazai ta Jihohi ta fara neman maniyyatan da su fara ajiye N8.5m.

Kara karanta wannan

ASUU ta zargi gwamnati da gaza biyan bukatunta, ana daura damarar yajin aiki

Jawabin kuma sanar da mayar da kudi 64,682 (Riyal Saudiyya 150) ga kowane mahajjacin Najeriya da ya halarci aikin hajjin 2023.

Sanarwar ta kara da cewa, an bayyana hakan ne a wata ganawar tattaunawa tsakanin NAHCON da ‘yan kungiyar masu yawon bude ido a Najeriya (PTOs).

2023: Ana shirin kara kudin aikin Hajji

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), ta bayyana cewa kamfanonin jiragen sama sun bukaci da a kara kudin aikin hajjin 2023

Shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan, ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sun bukaci da a kara kudin da $250 amma ya ce suna duba hanyoyin magance karin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.