Carbi: Za a Buga Muƙabala Mai Zafi Tsakanin Pantami da Idris Dutsen Tanshi

Carbi: Za a Buga Muƙabala Mai Zafi Tsakanin Pantami da Idris Dutsen Tanshi

  • Magana ta kara dawowa sabuwa musamman a kafafen sadarwa kan matsayin amfani da carbi a addinin Musulunci
  • Isa Ali Pantami ya ce amfani da carbi ba bidi'a ba ne kuma ya yi kira ga duk wanda yake ganin ba haka ba ne su yi muƙabala
  • A daya bangaren, Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya amsa gayyatar muƙabalar inda ya ambaci sharuda kan gudanar da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - An kara samun sabanin fahimta tsakanin Sheikh Isa Ali Pantami da Dakta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.

Malaman sun yi a sabani ne a kan matsayin amfani da carbi wanda har Sheikh Isa Pantami ya nemi a zauna a yi muƙabala.

Kara karanta wannan

Farfesa Pantami ya fadi matsayar musulunci kan ba shugabanni rigar kariya

Pantami|Dutsen Tanshi
Dr Idris ya amsa gayyatar mukabala da Sheikh Pantami. Hoto: Dutsen Tanshi Majlis Bauchi|Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Sheikh Idris Abdulaziz ya amince da yin muƙabalar a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin amfani da carbi a Musulunci

Sheikh Isa Ali Pantami ya ce amfani da carbi ba bidi'a ba ne a addini duk da cewa shi ba shi da carbi ko daya a duniya.

Isa Pantami ya kuma yi kira ga duk wanda yake da sabanin fahimta a kan haka da su yi mukabala domin baje hujjoji.

Muƙabala tsakanin Pantami da Dutsen Tanshi

Biyo bayan maganar Sheikh Pantami, Dakta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya ce ya karbi tayin muƙabalar.

Dakta Idris ya bayyana cewa ya karbi tayin muƙabalar ne domin fito da wasu hujjoji ga Sheikh Isa Ali Pantami.

A ina za a yi muƙabala kan carbi?

A bayanin da Sheikh Pantami ya yi, ya ce duk wanda ya karbi gayyatar zai zo birnin tarayya Abuja ne domin a yi muƙabalar.

Kara karanta wannan

'Ba ni kadai ba ne', Sheikh Gumi ya fadi wadanda ke raka shi wurin yan bindiga

Sai dai Dutsen Tanshi ya ce shi ba zai je masallacin Abuja ba kamar yadda Pantami ba zai zo masallacinsa ba, ya ce sai dai a hadu a kafar sadarwa.

A yanzu haka dai kallo ya koma kan Isa Ali Pantami domin ganin martanin da zai yi a kan amsa gayyatar da Dutsen Tanshi ya yi.

Shugaban Izala a Kebbi ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa a makon da ya wuce kungiyar Izala da Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ke jagoranta ta sanar da rasuwar shugaban gudanarwanta.

Rahotanni da suka fito sun nuna cewa Sheikh Shua'ibu Muhammad Sarkin Fawa ya rasu ne bayan jinya a gadon asibiti a Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng