Mukabala: Abduljabbar bai kai a yi masa gangami ba, in ji Sheikh Khalil

Mukabala: Abduljabbar bai kai a yi masa gangami ba, in ji Sheikh Khalil

- Sheikh Ibrahim Khalil, shugaban malaman arewa maso yamma yace darajar Abduljabbar bata kai a yi masa gangami ba

- Sheik Khalil yace kimarsa bata kai ba, hakan ne yasa mai Alfarma sarkin Musulmi ya ki turo wakilansa

- Idan zamu tuna Gwamna Abdullahi Ganduje ya haramtawa Sheikh Kabara wa'azi sakamakon wasu fatawoyin da yake badawa

Shugaban malamai na arewa maso yamma, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sanar da cewa kima da darajar Malam Abduljabbar Kabara basu kai ga malamai su yi masa gangamin taron dangi ba.

Sheikh Khalil ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da jaridar Leadership kan abinda ke faruwa tsakanin Abduljabbar da gwamnatin Kano.

Tun farko dai Ganduje ya haramtawa malamin yin wa'azi sakamakon zargin da da ake yi da bayar da wasu fatawoyi da suka sabawa koyarwar addini.

Malamin yace rashin darajar ne yasa Sarki Musulmi ya ki tura wakilan JNI wurin mukabalar.

KU KARANTA: Fani-Kayode ga Gumi: Kada ka saka Najeriya cikin rikici mai wuyar karewa da tsokacinka

Mukabala: Abduljabbar bai kai a yi masa gangami ba, in ji Sheikh Khalil
Mukabala: Abduljabbar bai kai a yi masa gangami ba, in ji Sheikh Khalil. Hoto daga @Leadership
Asali: Twitter

“Shi Malam Abduljabbar bai kai matsayin da za a yi masa wannan gangamin ba. Matsayinsa da martabarsa da kimarsa ba su kai inda za a yi masa wannan gangami ba,” a cewar Malam Khalil.

KU KARANTA: Tsohuwar matar Fani-Kayode ta maka shi gaban kotu, tana son karbar 'ya'yansu

A wani labari na daban, jiragen sama da ke samar da makamai tare da abinci ga 'yan bindiga shine babban dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta hana jiragen sama bi ta jihar Zamfara, an gano hakan a ranar Laraba.

Baya ga haka, ana amfani da jiragen saman wurin safarar zinarin da aka haka ba bisa ka'ida ba a jihar. Gwamnatiin tarayya ta haramtawa jiragen sama bi ta jihar Zamfara a ranar Talata bayan taron da aka yi na tsaron kasa.

Ta kara da haramta dukkan hakar ma'adanai na jihar har sai baba ta gani, The Nation ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng