Ana Tsaka da Ibada, Malamin Addini Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Jihar Borno

Ana Tsaka da Ibada, Malamin Addini Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Jihar Borno

  • Mutane sun shiga alhini a yayin da aka sanar da labarin rasuwar wani malamin addinin kirista a Maiduguri, babban birnin jihar Borno
  • Alaku Vincent na cocin Brethren (EYN) Moduganari da ke Maiduguri, ya fadi ya mutu a yayin bikin sadaukarwa da ake yiwa yara a cocin
  • Yayin da ba a bayyana musabbabin mutuwarsa ba, sakataren cocin Brothers of Nigeria, Timothy Hammajam, ya yi karin haske kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - An shiga cikin tsananin firgici a cocin Brethren (EYN) Moduganari da ke Maiduguri, babban birnin Borno, lokacin da Rabaran Alaku Vincent ya yanke jiki ya fadi matacce.

An rahoto cewa malamin addinin ya yanke jiki ya fadi lokacin da ake tsaka da bikin sadaukarwar da ake yiwa yara a cocin a ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Rai ɓakon duniya: Ministar Buhari ta yi babban rashin ɗanta 1 tilo a duniya

Malamin addinin Kirista ya yanke jiki ya fadi matacce ana tsaka da ibada a Borno
An rahoto cewa wani malamin addini ya yanke jiki ya fadi matacce a jihar Borno. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Malamin addini ya mutu a jihar Borno

A cewar rahotanni da jaridar The Punch ta fitar a ranar Litinin, Rabaran Vincent na cikin bikin ne lokacin da ya fadi kasa tare da suma nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce duk wani kokari na ganin an farfado da limamcin cocin ya ci tura, inda jim kadan aka tabbatar da mutuwarsa a taron ibadar na ranar Lahadi.

Har ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a bayyana musabbabin mutuwar a hukumance ba, sai dai ‘yan coci da abokan aikinsa, sun bayyana alhininsu a kafafen sada zumunta.

"Za mu yi kewarka" - Hammajam

Sakataren gunduma na cocin Brothers of Nigeria, Timothy Hammajam, a cikin wani sakon Facebook, ya bayyana marigayin a matsayin "shugaba mai hangen nesa kuma mai da hankali."

Kara karanta wannan

Sauye sauye a majalisar ministoci: Tinubu zai saki sunayen ministocin da zai kora

Hammajam ya bayyana cewa:

"Raraban Alaku Vincent (KZ Master) Jagora ne mai hangen nesa. Ubangiji ya sa ka kwanta cikin salama. 'Yan ajin KBC DCM 2003 za su yi kewarka da kuma kalaman dattakonka.
“Ubangiji ya tausashi EYN da iyalanka. Ka ci gaba da kwanciya cikin salama har mu zo mu tarar da kai."

Benuwai: Mutuwar fasto ta girgiza mutane

A wani labarin, mun ruwaito cewa ana zargin tsawa ta kashe babban malamin cocin St. Joseph Catholic da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benuwai, Rabaran Faustinus Gundu.

Rundunar 'yan sandan jihar Benuwai ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce bincike ne kaɗai zai gano abin da ya kashe Faston ba wai hasashen mutane ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.