Wani malamin coci ya yanke jiki ya mutu yana tsakiyar ibada a coci
- Wani limamin coci ya yanke jiki ya fadi matacce a lokacin da yake cikin wa’azi a Douala, kasar Kamaru
- A cikin wani bidiyo da Chidi Odinkalu ya wallafa, ya dan huta kadan kafin ya yanke jiki yayinda yake cikin wa’azi
- Masu amfani da shafin soshiya midiya sun je shafin Twitter domin fadin ra’ayinsu kan al’amarin
Wani lamari na bakin ciki ya afku a kasar Kamaru lokacin da wani limamin coci mai suna Father Jude ya yanke jiki ya fadi matacce a lokacin da yake wa’azi.
Wani tsohon Shugaban hukumar kare hakkin bil adam na kasa, Chidi Odinkalu ne ya wallafa bidiyon a shafin Twitter.
Odinkalu ya rubuta: “Rev. Fr Jude., CMA, daraktan CMA Deido, a babbar birnin Kamaru, Douala, na tsaka da wa’azi a cikin dandazon al’umma a yau lokacin da wannan faru. Allah ya ji kan shi.”
Mutumin, wanda ya kasance sanye da takunkumin fuska, ya dan dakata na dan lokaci sannan ya yanke jiki ya fadi. Sauran limaman cocin sun yi gaggawan kai masa agaji amma ya mutu.
Reverend Father Jude ya kasance daraktan kungiyar limaman Katolika a Douala, kasar Kamaru.
KU KARANTA KUMA: FG za ta kara wa'adin shirin daukar mutane 77400 aiki a Nigeria
Wasu masu amfani da shafin Twitter sun bayyana ra’ayinsu game da lamarin.
Wani mai amfani da Twitter @OYEDEJI ya rubuta: “Shin kun lura wani mutum na share gumi daga fuskarshi saboda dakin ya dauki dumi, sannan kuma ga takunkumin fuska a sanye. Eh, tabbass yana da muhimmanci. Shiyasa zan cire takunkumin fuskana idan naga bana iya numfashi da kyau idan ina sanye dashi. Rai daya ne!”
Da yake martani ga @OYEDEJI, @divergentscou ya rubuta: “Takunkumin fuska ba zai zama ainahin abunda ya haddasa hakan ba, amma na amince da kai, yana iya kasancewa daga cikin abunda ya haddasa hakan.
“Na lura da idonsa sau da dama, akwai alamu sosai da suka nuna faruwan haka. Allah ya ji kansa. Sanya takunkumin fuskarka. Ka tsira.”
@Ote_nkwu ya rubuta: “Da nake a coci da dafen nan, wani tunani ya zo zuciya... Toh idan wannan limamin ya fadi fa? Sai gashi ya faru a wani wuri daban.”
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng