Shahararren Mawakin Bishara Na Najeriya Ya Yanke Jiki, Ya Mutu A Gidansa A Legas

Shahararren Mawakin Bishara Na Najeriya Ya Yanke Jiki, Ya Mutu A Gidansa A Legas

  • Allah ya yi wa fittacen mawakin bishara na Najeriya, Sammie Okposo rasuwa a Legas
  • Rahatanni sun bayyana cewa mawakin ya yanke jiki a gidansa ya fadi matacce ne a safiyar yau
  • Okposo ya fara waka ne a matsayin furodusa a sauti a masana'antar Nollywood a shekarar 1992 daga nan ya samu bunkasa

Jihar Legas - Shahararen mawakin bishara na Najeriya, ya rasu yana da shekaru 51 a duniya.

This Day ta rahoto cewa furodusa, ID Cabasa, ya ce mawakin ya yanke jiki ya fadi a gidansa da ke Legas a ranar Juma'a.

Sammie Okposo
Shahararren Mawakin Bishara Na Najeriya Ya Yanke Jiki, Ya Mutu A Gidansa A Legas. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Babu cikakken bayani game da rasuwarsa a lokacin hada wannan rahoton.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu cikin danginsa da The Cable Lifestyle ta tuntuba game da lamarin sun ce ba za su iya magana a yanzu ba.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Gwamna da Karbar Dala Miliyan 28 Domin Bata ‘Dan Takarar Shugaban Kasa

A watan Mayun wannan shekarar, ya tsira bayan hatsarin mota ta ritsa da shi yayin da ya ke tuki a gadar 3rd mainland a Legas, rahoton Daily Trust.

Bayan ya yi fice, Sammie Okposo ya kafa kansa a matsayin mawakin kasa da kasa na bishara.

Kuma shi furodusa ne kuma shugaban kamfanin Zamar Entertainment.

Mawakin ya fitar da kunshin wakokinsa na farko mai suna 'Addicted' a 2004.

Ya yi wakar hadin gwiwa tare da wasu mawakan da dama a bangaren bishara da wasu daban.

Manajan Okposo ya tabbatar da rasuwarsa

Manajan ayyukansa, Hillary Vincent, ya tabbatarwa da The Punch rasuwa Okposo ta hirar tarho.

Da ya ke amsa tambayoyin da aka masa, ya ce:

"Eh, da gaske ne. Ya faru da safiyar yau."

Amma, Vincent bai zurfafa bayani kan rasuwar mawakin ba domin bai bayyana sillar rasuwarsa ba.

Takaitaccen tarihin Okposo

Sammie Okposo ya fara sana'arsa a waka a matsayin furodusa na sauti a masana'antar fina-finai Nollywood a 1992.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: FG Ta Kwato $1b Daga Masu Satar Kudin Najeriya Tun Daga 2015

Ya yi fice a cikin jarumai da furodusoshin Nollywood.

Daga baya ya fara bunkasa a lokacin da ya fara shirya Sammie Okposo Praise, wata kafa a ake kawo sabbin mawakan bishara na Najeriya su nuna bajintarsu.

Mawakin haifafan Neja-Delta ya yi fice saboda fitar da wakarsa daga coci.

Ya fitar da kunshin wakokinsa na farko mai taken 'Unconditional Love' a shekarar 2000.

Ifeanyi Adeleke, Dan Fitaccen Mawaki Davido, Ya Rasu

Hankulan yan uwa da masoya da abokan arziki na mawakin Najeriya, David Adeleke da aka fi sani da 'Davido' sun tashi bayan samun labarin rasuwar dansa. Ifeanyi.

Kamar yadda rahotannu suka bayyana, yaron ya rasu ne cikin rafin wanka na shakatawa da ke cikin gidansa a unguwar Banana Island, jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel