Rigima Ta Kaure Tsakanin Gwamnan Neja da 'Yan Kwadago, Bayanai Sun Fito
- An samu musayar yawu tsakanin gwamnatin jihar Neja da kungiyar 'yan kwadago kan bukatun da malamai suka gabatarwa gwamnatin
- Kungiyar malaman jihar ta TUC ta lissafa wasu bukatu na malaman firamare da sakandare da har yanzu gwamnatin Neja ba ta cika su ba
- Sai dai gwamnatin jihar ta bakin Dakta Mustapha Ibrahim ta nuna cewa muhimmancin bukatun malaman bai kai yadda TUC ke rurutawa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - An samu wata 'yar hatsaniya a lokacin bikin ranar malamai ta duniya na 2024 a cibiyar taro ta Mai shari'a Idris Legbo Kutigi da ke a jihar Neja a ranar Asabar.
Babban darakta na cibiyar bunkasa ilimi ta jihar Neja, Dakta Mustapha Ibrahim Lemu, ya yi watsi da korafe-korafen jin dadin malamai da 'yan kwadago suka gabatar.
Dakta Mustapha wanda ya gabatar da makala mai taken 'mutunta muryoyin malamai ga bunkasa ilimi' ya ce walwalar malamai ba ta muhimmancin da kungiyar NUT ke ikirari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman daraktan cibiyar ya jawo ce-ce-ku-ce tare da musayar kalamai masu zafi inji rahoton Daily Trust.
Malamai sun soki gwamnatin Neja
A jawabinsa na maraba, shugaban kungiyar malaman makarantun firamare, Akayago Adamu Mohammed, ya koka da yadda gwamnatin Neja ta tauye hakkokin malaman firamare.
Shugaban NUT ya lissafa kalubalen da malaman firamare ke fuskanta da suka hada da rashin aiwatar da alawus malaman makarantun sakandare tun daga shekarar 2018.
Sauran kalubalen sun hada da tabarbarewar ci gaban wadanda ke mataki na 16, rashin aiwatar da karin girma a kowace shekara tun daga shekarar 2018.
Ya ce har yanzu jihar ba ta shiga jerin jihohin da suka aiwatar da tsawaita wa’adin ritayar malaman makaranta zuwa shekaru 40 ba.
Dakta Mohammed ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta magance wadannan matsaloli tare da duba albashin malaman bisa la’akari da tsadar rayuwa da ake ciki.
Neja: Gwamnati ta soki malamai
To sai dai Dakta Lemu ya zargi kungiyar NUT da kambama walwalar malamai da ya wuce kima, inda ya bukaci su kara himma kawai wajen ba da ilimi mai kyau tare da jiran ladansu.
Dakta Lemu ya yi nuni da cewa maganganun malaman a yanzu ba su da wata fa'ida kasancewar gwamnatin jihar ta riga da ta sauke nauyin da ke kanta kuma tana kokarin biyan bukatunsu.
A jawabinsa, shugaban kungiyar kwadago NLC na jihar, Idris Lafene ya ce jin dadin malamai na da matukar muhimmanci idan har ana son a samu ingantaccen ilimi.
Malaman Neja ba su da kwarewa?
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumarilimin bai daya ta Neja ta bayyana cewa da akwai wadansu malamai da daman gaske a jihar da ba su iya karatu ko rubutu ba.
Hukumar ta bayyana cewa ta kashe kudade wajen saka yara 250 a makaranta amma daga bisani bayanai suka nuna babu abin da yaran suka koya saboda rashin kwarewar malaman.
Asali: Legit.ng