Kungiyar NUT ta roki gwamnatin Rivers da ta biya malaman jihar Albashi da hakkokinsu

Kungiyar NUT ta roki gwamnatin Rivers da ta biya malaman jihar Albashi da hakkokinsu

- Malamai a jihar Rivers sun roki gwamnatin jihar da ta biya su basussukan albashin da suke bi

- Sun bukaci da a kara masu girma a wajen aiki tare da kaddamar da albashin malaman da aka karawa matsayi a 2009

- Haka zalika sun bayyana bukatar su ta a biya yan fansho da giratuti hakkonkin

Malaman firamare da na sakandire a jihar Rivers sun roki gwamnatin jihar da ta biya su hakkokin su na Albashi da wasu alawus alawus da gwamnatin ta gaza biyansu.

Haka zalika kungiyar malamai ta kasa NUT reshen jihar Rivers sun bukaci gwamnatin jihar da ta cika alkawuran da ta daukarwa malamai.

A cikin wata takarda dauke da bukatu 10 na malaman, wacce shugaban kungiyar NUT na jihar, Mr. Kpogene Lucky ya karanta, a garin Fatakwal, kungiyar tace akwai babban muhimmanci ga gwamnati ta waiwayi walwalar malaman jihar.

Kungiyar NUT ta roki gwamnatin Rivers da ta biya malaman jihar Albashi da hakkokinsu
Kungiyar NUT ta roki gwamnatin Rivers da ta biya malaman jihar Albashi da hakkokinsu
Asali: Depositphotos

Sanarwar ta ce: "Bari na fadi wannan maganar da babbar murya, kungiyar malamai ta jihar Rivers na da hakoran tauna tsakuwa don aya taji tsoro, don haka bai kamata a dauketa kamar wata sanuwar ba, ko ma a kaita makurar hakuri.

KARANTA WANNAN: Ma'aikata 4,042 da gwamnatin Kaduna ta kora daga aiki sun maka El-Rufai kotu

"Shin ta yaya malamai za su ci gaba da magiya ga gwamnati na ta kara masu girma wajen aiki da kuma biyansu hakkokinsu tun a 2009 har zuwa yau?

"Sauran bukatun kungiyar sun hada da kaddamar da karin albashi ga wadanda aka yiwa karin matsayi daga 2009 zuwa 2010, biyan basussukan albashi na watan Febreru da na Mayu n 2016 ga malamai da matsalar albashin ta shafa, biyan alawus alawus ga malaman da ke koyarwa a yankunan karkara."

Daga karshe shugaban kungiyar NUT reshen jihar Rivers, ya ce biyu daga cikin bukatun kungiyar sun hada da sakin takardun shaidar karin girma ga malamai na 2011, 2012 da 2013 da ke koyarwa karkashin makarantun sakandire tare da kuma biyan fansho da giratuti ga malaman da suka yi ritaya.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.naija.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng