Wasu malamai a Jihar Neja ba su iya rubutu da karatu ba, Shugaban Hukumar Ilimin jihar
- Dalibai 21 ne kacal suka ci jarrabawar shiga sakandare
- Bincike ya nuna kaso mafi yawa na malaman firamare a jihar ba su iya karatu da rubutu ba
- Wadanda suke da kokarin ma, galibinsu ba su da dabarun koyarwa.
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya a Jihar Neja, Isah Adamu, ya bayyana cewa da akwai wadansu malamai da daman gaske a jihar da ba su iya karatu ko rubutu ba.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin taron lalubo yadda za a farfado da ilimin firamare a jihar.
Ya ce an kira taron da zimmar samun goyon bayan masu ruwa da tsaki a fannin ilimi ta yadda za a shawo kan kalubalen da bangaren ilimin firamaren ke fuskanta a jihar.
A cewarsa, taron ya zama wajibi a yi shi bayan hukumar ta kashe kudade wajen saka yara 250 a makaranta amma daga bisani bayanai suka nuna babu abin da yaran suka tabuka a harkar karatu.
KU KARANTA: Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi
KU DUBA: Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah
Yace:
“Bayan mun samu marawar bayan gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello mun saka wa kanmu ajendar aiki wurjanjan domin ganin mun inganta ilimin firamare a Jihar Neja.
“Aikin farko da muka fara yi shi ne mun fita rangadin jihar baki daya domin duba yadda halin da makarantun suke ciki. Abin da muka tarar a kasa ba mai kyau ba ne. Halin da wasu makarnatun ke ciki abin takaici ne sosai; za ka tarar malamai ba sa iya bayar da karatu yadda ya dace, sannan mafi munin ma akwai malaman da ba sa iya karatu ko rubutu.
“Domin fahimtar hakikanin lamarin, mun kafa kwamitin da ya binciki harkar koyarwa da gudanarwa a dukkanin kananan hukumomin jihar 25.
“Rahoton kwamitin ya gano cewa da dama daga cikin malaman ba sa iya karatu ko rubutu."
Ya kara da cewa a jarrabawar shiga makarantun sakandare na tarayya dalibai 21 ne kacal cikin 250 suka ci jarrabawar.
A nasa jawabin, gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Bello, ya koka kan matukar lalacewar ilimin firamare a jihar.
Gwamnan wanda mataimakinsa Ahmed Ketso, ya wakilta ya bukaci mahalarta taron da lallai su lalubo hanyoyin inganta harkar ilimin firamare masu dorewa a jihar.
A bangare guda, gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa ta fara tattaunawar neman masalaha da yan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina ƙaramar hukumar Rafi jihar Neja.
Gwamnatin tace ta fahinci an fara tattauna wa tsakanin yan bindigan da iyayen yaran, amma tace ita ba zata biya ko sisi da sunan kuɗin fansa ba.
Mataimakin gwamnan jihar, Muhammad Ketso, shine ya bayyana haka a Minna Ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai, kamar yadda punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng