Kudurin doka kan karawa malamai wa'adin shekarun ritaya ya wuce karatu na biyu
- Kudurin doka don kara yawan shekarun ritayar malamai daga shekaru 60 zuwa 70, ya wuce karatu na biyu a majalisar dokoki ta jihar Adamawa
- Abdullahi Yapak (APC - Verre) ne ya gabatar da kurin a gaban majalisar, wanda kuma shine shugaban kwamitin tsayayyu kan Ilimi na majalisar
- Kudurin dokar, ya bukaci karin kaso 10 na albashi a matsayin alawus alawus ga malaman da aka tura garuruwan da ke a wajen shelkwatar kwananan hukumominsu
Kudurin doka don kara yawan adadin shekarun da malaman firmare da na sakandire ke yi kafin ritayarsu daga shekaru 60 zuwa 70, ya wuce karatu na biyu a majalisar dokoki ta jihar Adamawa.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Abdullahi Yapak (APC - Verre) ne ya gabatar da kurin a gaban majalisar, wanda kuma shine shugaban kwamitin tsayayyu kan Ilimi na majalisar.
Da ya ke jawabi a ranar Talata, a zaman da majalisar ta gudanar karkashin jagorancin kakakin majalisar, Alhaji Kabiru Mijinyawa, Yapak ya ce kudirin dokar, zai taimaka wajen dawo da martabar ilimi a makarantun gwamnati da kuma karfafa guiwar malamai wajen koyar da dalibai iya karfinsu.
KARANTA WANNAN: Sabon tarihi: Ilhan Omar, Rashida Tlaib sun zama Musulmai na farko a majalisar dattijan Amurka
A gudunmowarsa ga wannan kudurin doka, Sunday Peter (APC - Guyuk), ya jinjinawa wanda ya gabatar da kudurin, yana mai karacwa da cewa irin wannan kudurin dokar ne zai dawo da martabar ilimi a makarantun gwamnati.
Peter ya kara da ewa, akwai bukatar bunkasa walwalar malamai.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ci gaba da ruwaito cewa kudurin dokar, ya bukaci karin kaso 10 na albashi a matsayin alawus alawus ga malaman da aka tura garuruwan da ke a wajen shelkwatar kwananan hukumominsu.
Kudurin dokar ya kuma bayyana bukatar samar da karin malamai da kuma bukatar samar da kwamiti na musamman kan ilimin jama'a, da zai hada da babban malami da kuma shuwagabannin gargajiya guda biyu a cikin kowacce makaranta.
Daga karshe, kakin majalisar, ya tura kudirin dokar zuwa ga kwmaitin ilimi na majalisar don yin duba da sake gyare gyare, don karanta shi a zama na gaba.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng