Masanin Tattalin Arziki Ya Fadi Dabarar da Za Ta Karya Farashin Kayan Abinci Farat Daya
- Kalu Aja ya yi suna wajen yin sharhi da fashin baki a kan sha’anin tattalin arziki a Najeriya da duniya
- Masanin tattalin ya na ganin idan ana bukatar abinci ya sauko, sai an saidawa ‘yan kasuwa $1 a N200
- Aja ya ce karya dala domin kawo kayan abinci daga kasashen waje bai bukatar bata lokaci ko kadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Kalu Aja wanda masani ne a harkar tattalin arzikin Najeriya ya kawo shawara domin kawo saukin halin da ake ciki.
A halin yanzu mafi yawan al’umma su na kuka musamman a game da tsadar da kayan masarufi da abinci su ka yi a Najeriya.
Kalu Aja a shafinsa na X watau Twitter, ya karfafa maganar cire harajin VAT daga abinci domin a samu saukin farashi a kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masanin ya kafa hujja da cewa gwamnatin Najeriya ta na samun mafi yawan kudin shigar ta ne daga mai, harajin VAT da fetur.
Sauran hanyoyin samun kudin su ne hukumar kwastam da ke karbar haraji a kan kayan da aka shigo da su daga kasashen waje.
Yadda abinci zai sauko a Najeriya
Idan ana so abinci ya yi sauki, Mista Kalu Aja ya nemi gwamnatin Bola Tinubu ta saida Dala a kan N200 a shigo da kayan abinci.
Gwamnan CBN ya daidaita farashin kudin kasashen waje da ya shiga ofis, Aja ya na so a maido tallafin Dala a sayo abinci a ketare.
A shigo da kayan abinci na watanni 3
Masanin ya na so a bude wannan kofar na tsawon watanni uku ta yadda za a samu saukin abinci kuma a iya tara kudin shiga.
A cewarsa, idan aka yi hakan, abin da gwamnatin tarayya za ta rasa shi ne N500bn da ya kamata kwastam ta samu a watanni uku.
Sannan ya kara da cewa za a iya daukar wannan mataki ko a yau ba tare da jiran wata amincewar ‘yan majalisar tarayya ba.
Rangwamen Dala zai rage tsadar abinci
"Wannan zai karya farashin abinci nan ta ke. Kayan abinci shi ne 51% na CPI, sauke farashin abinci zai kawo saukin hauhawar farashin kaya.
A bayanin da ya yi a dandalin sada zumuntan, ya ce akasarin magidanta su na kashe 57% na kudin su ne a kan kayan abinci.
- Kalu Aja
Shinkafa za ta fadi a kasuwa
Rahoto ya zo cewa ana kokarin a sauke farashin shinkafa a jihohi. Gwamnatin tarayya ta fara shirin saida buhuna da rahusa.
Ma'aikatar noma da samar da abinci ta ce za a rika sayar da buhun shinkafa ne a kan N40,000 domin a kawowa al'umma rangwame.
Asali: Legit.ng