Iran vs Isra'ila: Gwamnati Ta Aika Sakon Gaggawa ga 'Yan Najeriya Mazauna Lebanon

Iran vs Isra'ila: Gwamnati Ta Aika Sakon Gaggawa ga 'Yan Najeriya Mazauna Lebanon

  • Ana ci gaba da zaman dari dari a Lebanon yayin da takun saka tsakanin Isra'ila da Iran ya a'azzara musamman bayan harin baya bayan nan
  • Gwamnatin tarayya ta bukaci 'yan Najeriya mazauna Lebanon da su gaggauta dawowa gida tun jiragen kasuwa na aiki kafin lamura su munana
  • Hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) ta ce tana sa ido sosai kan rigingimun da ke faruwa a Gabas ta tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya mazauna Lebanon da su dawo gida duba da ta'azzarar tashe tashen hankula a kasar da kuma Gabas ta Tsakiya.

Hukumar NiDCOM ta fitar da sakon ne yayin da rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da Hizbullah ya ta'azzara wanda ya haifar da tashin hankaluna a wasu sassan kasar Lebanon.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 da daina aiki, 'dan asalin Kano ya tuko jirgin Emirates zuwa Najeriya

Gwamnati ta yi magana kan tashe tashen hankula a kasashen Gabas ta Tsakiya
Gwamnati ta bukaci 'yan Najeriya mazauna Lebanon su dawo gida. Hoto: @nidcom_gov
Asali: Twitter

An gargadi 'yan Najeriya da ke Lebanon

Jaridar Leadership ta rahoto NiDCOM ta shawarci 'yan Najeriya da su baro kasar tun da jiragen kasuwanci na kan aiki, duba da yanayin rashin tabbas na tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan sashen yada labarai, hulda da jama’a a hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), Abdur-Rahman Balogun ne ya fitar da sanarwar gargadin.

Abdur-Rahman Balogun ya ce:

"Dangane da hare-haren da Isra'ila ke kai wa sojojin Hezbollah da sauran yankunan Lebanon, muna ba 'yan Najeriya mazauna Lebanon shawarar barin kasar tun girma da arziki."

Wane hali 'yan Najeriya ke ciki a Lebanon?

Hukumar NiDCOM ta bayyana cewa, 'yan Najeriya da dama sun kaura daga yankunan da ke fama da tashe tashen hankula musamman a kudancin Lebanon zuwa wurare masu tsaro.

"An sanar da mu cewa yawancin 'yan Najeriya sun koma yankunan da ke da tsaro, amma muna ci gaba da rokon su da su yi taka tsantsan har sai an tsagaita bude wuta."

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi sababbin dokoki, ta hana mata hawa Keke Napep daga karfe 10

- A cewar Balogun.

Hukumar NiDCOM ta kuma tabbatar wa jama'a cewa kawo yanzu babu wani dan Najeriya da aka jikkata a rikicin, inji rahoton NTA.

Gwamnatin Najeriya na sa ido sosai kan lamarin tare da jaddada cewa kare lafiyar al’ummarta da kuma jin dadinsu ne babban abin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sa a gaba.

Iran ta kai mummunan hari Isra'ila

A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta harba akalla makamai masu linzami 180 cikin kasar Isra'ila a ranar Talata, lamarin da ke barazanar mayar da Gabas ta Tsakiya wani yanki na yaki.

Iran ta ce harin na ramuwar gayya ne kan wasu munanan hare-hare da Isra'ila ta kai kan sojojin Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran a Lebanon da kuma kashe Hassan Nasrallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.