Gwamnati Ta Dauki Matakin Karya Farashin Abinci, Shinkafa Za Ta Sauko a Jihohi

Gwamnati Ta Dauki Matakin Karya Farashin Abinci, Shinkafa Za Ta Sauko a Jihohi

  • Gwamnatin tarayya karkashin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki matakin sauko da farashin shinkafa a jihohin Najeriya
  • An ruwaito cewa ma'aikatar noma da samar da abinci ce ta bayyana haka ga manema labarai a babban birnin tarayya Abuja
  • A karon farko, za a kaddamar da shirin a jihohin Kano, Legas da Borno domin saukakawa al'umma kan halin rayuwa da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ma'aikatar noma da samar da abinci ta bayyana shirin karya farashin shinkafa a jihohin Najeriya.

Ma'aikatar tarayyan ta ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na samar da saukin rayuwa.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Bola Tinubu
Gwamnati za ta samar da shinkafa a jihohi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Ahmad Sabo
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a ranar Litinin ne ma'ikatar noma da samar da abinci ta kasa ta bayyana lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shinkafar da za a kai jihohin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a kai shinkafa ton 30,000 ne a jihohi yayin fara shirin karya farashin.

Hakan kuma na nuni da cewa za a tura tirelar shinkafa 1,000 zuwa jihohi inda kowace tirela za ta dauki buhun shinkafa 600.

Jihohin da za a karya farashin abinci

Wani jami'in ma'aikatar noma da samar da abinci ya bayyana cewa za a zabi wasu jihohi ne a karon farko.

A karkashin haka ya tabbatar da cewa za a fara shirin ne a jihohin Kano, Borno da Legas a yanzu haka.

Yadda za a karya farashin abinci

Ma'aikatar noma ta bayyana cewa za a rika sayar da buhun shinkafa ne a kan N40,000 maimakon N90,000 ko 100,000 da ake sayarwa a kasuwa.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da murnar ranar ƴanci: Gwamnatin tarayya ta karawa ƴan fansho albashi

Jami'i a ma'aikatar noma ya ce a yanzu haka suna cigaba da sayar da buhun shinkafa a kan N40,000 a birnin tarayya Abuja.

'Yan Najeriya sun yiwa Tinubu raddi

A wani rahoton, kun ji cewa ranar 1 ga watan Oktoba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga yan kasa kan yanci da aka samu daga turawan Birtaniya.

Sai dai jawabin shugaban kasar na wannar shekarar ya jawo suka sosai kan cewa bai yi magana kan manyan damuwowin Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng