An Shiga Tashin Hankali a Yobe, Sufetan 'Yan Sanda Ya Kashe Wani Mutumi kan N200
- An samu wani mummunan lamari na kisan gilla a Yobe, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce tare da neman a gaggauta daukar mataki
- A ranar Lahadi, 29 ga Satumbar 2024 ne aka rahoto cewa wani sufetan 'yan sanda a Damaturu ya kashe wani farar hula kan N200
- An ce Sufeta Mohammed Bulama ya yanke wuyan AbdulMalik Galadima saboda ya hana shi cin hancin N200 da ya tambaye shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Al'ummar garin Zango da ke gundumar Nasarawa, jihar Yobe sun shiga cikin tashin hankali bayan wani sufetan 'yan sanda ya kashe wani mutumi a kan N200.
An rahoto cewa sufetan 'yan sanda mai suna Mohammed Bulama ya dabawa AbdulMalik Galadima wuka har lahira saboda ya hana shi cin hancin N200.
Yobe: Sufetan 'yan sanda ya kashe farar hula
Zagazola Makama, wanda ya wallafa labarin a shafinsa na X, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a Zango, unguwar Nasarawa a jihar Yobe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A ranar Lahadi, 29 ga Satumbar 2024, Sufeta Mohammed Bulama na rundunar MP da ke Damaturu ya yi ajalin wani farar hula, AbdulMalik Dauda Galadima, a Zango, gundumar Nasarawa.
"A cewar shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru da misalin karfe 5:05 na yamma inda Sufeta Bulama ya nemi Galadima ya ba shi cin hancin N200."
- A cewar rahoton Makama.
Yadda dan sanda ya kashe Galadima
Rahoton ya nuna cewa Sufeta Bulama ya fara tayar da jijiyoyin wuya lokacin da Galadima ya shaida masa cewa ba shi da N200 da zai bayar a lokacin.
“Lokacin da marigayin ya bayyana cewa babu kudi a tare da shi, sai aka ce dan sandan ya fara zage zage tare da cin zarafin mutumin.
"A cikin wani mummunan lamari, aka yi zargin Sufeta Bulama ya yanke wuyan Galadima tare da daba masa wuka a kirji, wanda ya kai ga mutuwarsa nan take."
- A cewar rahoton.
Rahoton ya kara da cewa kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun bukaci a yi adalci da kuma bin diddigi daga hukumar 'yan sandan Yobe da ma ta kasa.
Dan sanda ya kashe dan acaba
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani dan sandan Najeriya mai karbar na goro ya kashe wani dan acaba a jihar Ebonyi saboda yaki bashi cin hancin N50.
Shaidun gani da ido sun ce 'yan sandan sun tare shi da daddare tare da neman cin hancin N50 amma ya ba su N20, lamarin da ya sa suka bude masa wuta da zai tafi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng