Yadda Dan sanda ya kashe dan acaba saboda ya hana shi cin hancin N100
Mazauna karamar hukumar Okota sun zargi jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya na jihar Legas da laifin kashe wani dan acaba mai suna Aliu Rafiu.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe Rafiu ne da safiyar ranar Laraba a kan hanyarsa ta zuwa aiki saboda ya ki bawa wani jami'in dan sanda cin hanci na Naira 100 kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Bidiyon yadda abin ya faru tuni ya karade shafukan sada zumunta.
Wani mazaunin unguwar, Adebayo Ishola ya yi bayyanin cewa masu sana'ar kabu-kabu da adaidaita sahu ne kawai aka bawa izinin bin hanyar da aka tsinci gawar Rafiu.
Ya ce saboda haka ne yasa 'yan sandan kan karbi cin hanci daga hannun masu babur indan sun bi hanyan.
Ishola ya ce wasu 'yan sanda biyu; Monday da Ekene ne suka cafke Rafiu sannan Monday ya buge shi da kulki a kansa.
DUBA WANNAN: An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila
Ishola ya ce: "Da safe ne muka ga gawa a kan titi tare da wani mai sana'r babur a wurin. Mai babur din ya ce wasu 'yan sanda biyu, Monday da Ekene ne suka kashe Rafiu.
"Wani mutum ya tabbatar da cewa ya gani Monday tare da marigayin. Sunyi kokarin karbar kudi daga hannunsa bayan sun cafke shi. Monday ya yi amfani da kotar bindigarsa ya bugi Rafiu a kai kuma nan take jini ya fara zuba.
"Suna ganin jinin ya cigaba da kwarara sai suka bar shi a kan titin suka shige caji ofis. Na ji wani mai mota da ya zai wuce a hanyar yana cewa Monday da Ekene ne suka kashe Rafiu."
Wani shaidan ganin ido wanda ya ce sunan sa Shola ya ce yana hanyarsa na zuwa aiki ne yayin da ya ga abinda 'yan sandan suka yiwa Rafiu.
Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Bala Elkana ya ce 'yan sanda ba su da hannu a rasuwar dan acabar.
Bala ya ce: "Rundunar 'yan sanda ta ga wani bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta inda ake ikirarin dan sanda ne ya kashe wani mai acaba. Wannan zargin ba gaskiya bane.
"A ranar 8 ga watan Mayun 2019 misalin karfe 6 na safiya a caji ofis na Ago-Okota 'yan sanda sun ji hayaniya daga waje hakan ya sa suka garzaya domin duba abinda ke faruwa. Da isar su sai suka ga wani dan acaba kwance cikin jini a kasa. Sun kai shi asibiti amma daga bisani ya rasu.
"Bayyanan da muka samu daga shaidan gani ido ya ce dan acabar ya yi hatsari ne da wata mota a kan titin Ago Palace inda wani mai mota kirar Toyota Camry ya buge dan acabar kuma ya tsere.
"A halin yanzu ana gudanar da bincike domin gano matukin motar domin ya fuskanci hukunci a kan abinda ya aikata."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng