Dan sanda mai neman na goro ya kashe dan achaba a jihar Ebonyi

Dan sanda mai neman na goro ya kashe dan achaba a jihar Ebonyi

Rahotanni sun kawo cewa a daren ranar Larba, wani jami’in dan sanda ya harbe dan achaba har lahira a hanyar water works dake jihar Ebonyi saboda yaki bashi cin hancin naira 50.

Jami’an yan sanda na hanyar water works dake jihar Ebonyi ne suka tsare dan achaban.

Wata majiya da abun ya faru akan idanunsu sunce dan achaban wanda ya kasance matashi na dauke da fasinja mace lokacin da jami’an yan sanda suka garkae shi, kamar yadda suka saba karban na goro daga hannun yan achaba da daddare a wannan waje.

“A lokacin da suka tsayar das hi, sun bukaci ya basu N50 kamar kullun amma zai ya basu N20 yayinda yayi kokarin tashin babur din nasa daya daga cikinsu ya bude mai wuta. Alburushin ya same shi a kai inda a take anan ya mutu,” inji idon shaidan.

Dan sanda mai neman na goro ya kashe dan achaba a jihar Ebonyi
Dan sanda mai neman na goro ya kashe dan achaba a jihar Ebonyi

Lamarin ya haddasa hargitsi a hanyar yayinda mazauna yankin suka tattaru sannan suka yi yunkurin lallasa jami’an. Suka kuma tayar da wuta ta hanyar amfani da tayoyi.

KU KARANTA KUMA: Aikin hadi-gwiwa: Sojoji da ‘Yan Sanda sun yi ram da ‘Yan bindiga a Najeriya

Sai dai zuwan wasu sabbin jami’an yan sanda ya takaita abun yayinda sukayi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa dandazon mutanen da kuma yin harbi a sama.

Sai dai babu bayani ko alburushin ya samu fasinjar da ya dauko.

A halin da ake ciki, Gwamna David Umahi ya bada umurnin kama jami’in dan sandan da aikata kisan. Ya kuma bada tabbacin cewa zaa kamanta adalci.

A wani lamari na daban, mun samu labari cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun damke wasu da ake zargi da ta tada fitina a Yankin Nasarawa. An kama wadannan mutanen ne a Garin Ugyi da ke cikin Karamar Hukumar Toto.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng