‘Ba Abin da Ya Dame Mu’: Turji Ya Magantu kan Kisan Halilu Sabubu, Ya Bugi Kirji

‘Ba Abin da Ya Dame Mu’: Turji Ya Magantu kan Kisan Halilu Sabubu, Ya Bugi Kirji

  • Kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya fitar da sabon bidiyo a jiya Litinin 30 ga watan Satumbar 2024 a jihar Zamfara
  • Dan ta'addan ya yi magana kan kisan Halilu Sabubu da sojoji suka yi inda ya bayyana shi a matsayin mai gidansu
  • Turji ya yi ta'aziyyar kisan Sabubu inda ya ce hakan kwata-kwata ba zai kashe musu guiwa ba idan ba a bar kashe musu yan uwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Rikakken dan ta'adda, Bello Turji ya sake fitar da wani sabon bidiyo bayan kisan Halilu Sabubu.

Turji ya bugi kirji inda ya yi ta'aziyya ga mai gidan nasa da rundunar sojojin Najeriya suka hallaka.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya saki sabon bidiyo, ya kafa sharudan zaman lafiya a Zamfara

Bello Turji ya yi magana bayan kisan Halilu Sabubu
Dan ta'adda, Bello Turji ya yi ta'azziyar mutuwar mai gidansa, Halilu Sabubu. Hoto: Buhari Abdulkadir.
Asali: Facebook

Turji ya yi magana kan kisan Sabubu

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da @The_HBMayana a wallafa a shafin X a yau Talata 1 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, Bello Turji ya ce ko kadan kisan mai gidan nasu ba zai rage musu karfin komai ba.

Turji ya ce kisan sai dai ya kara musu karsashi musamman yaran da ke tasowa domin cigaba da kai hare-hare.

Turji ya fadi hanyar zai dakile hare-hare

"Kachalla Halilu Sabubu ba shi ne na farko ba da aka kashe, an hallaka da dama a baya."
"Kisan Sabubu ba zai hana mu abin da muke yi ba har sai dai idan kun bar kashe yan uwanmu a Zamfara da Sokoto da Katsina da kuma Niger."
"Nufinku shi ne ku karar da kabilar Fulani a doron kasa kuma Allah yana cigaba da kare mu, ko da kun kashe mu ubangiji ne ya kaddara amma ba karfinku ba."

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Abin da Tinubu ya fada game da halin kunci, ya roki yan kasa

- Bello Turji

Sojoji sun yi magana kan Bello Turji

Kun ji cewa yayin da aka hallaka dan ta'adda, Halilu Sabubu, rundumar tsaro ta sha alwashin kawo karshen sauran yan bindiga.

Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce za su kawo karshen rikakken dan ta'adda, Bello Turji nan ba da jimawa ba.

Janar Musa ya kuma gargadi al'umma da ke taimakon yan bindiga ta bangarori da dama da su yi hankali da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.