Kai Tsaye: Yadda Zanga Zangar Adawa da Gwamnatin Tinubu Ke Gudana Ana Murnar Samun 'Yanci

Kai Tsaye: Yadda Zanga Zangar Adawa da Gwamnatin Tinubu Ke Gudana Ana Murnar Samun 'Yanci

A yau Talata 1 ga watan Oktoban 2024 yan Najeriya ke murnar cika shekaru 64 da kasar ta yi na samun yanci daga Burtaniya, sai dai bikin ya ci karo da cikas inda wasu matasa ke zanga-zangar adawa da gwamnatin Bola Tinubu.

Wannan shi ne karo na biyu da matasan ke yin zanga-zangar gama-gari tun bayan hawan Bola Tinubu bayan cika tituna a ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.

Ƴan daba sun mamaye filin zanga-zanga

Ƴan daba sun mamaye filin zanga-zangar da aka yi amfani da shi wajen zanga-zangar #EndadBadGovernance a watan Agusta a dandalin Pleasure Park da ke birnin Port-Harcourt babban birnin jihar Rivers. 

Ƴan daban ɗauke da bulalai sun mamaye filin inda suka ce ba su son wata zanga-zanga a jihar Rivers, cewar rahoton tashar Channels tv.

Ƴan barandan sun yi barazanar cewa za su lakaɗa duka ga duk wani ɗan jaridan da ya kuskura ya yi musu bidiyo.

Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga

Jami'an yan sandan kasar nan sun tarwatsa dandazon masu zanga-zanga da borkonon tsohuwa a Abuja.

Jama'ar kasar nan sun yi shirin bayyana rashin jin dadin manufofin gwamnati a ranar zagayowar murnar samun yanci.

Kafin a tarwatsa su dai, mutanen na dauke da kwalaye, inda su ke neman "a kawo ƙarshen rashin shugabanci nagari" tare da wake-waken "yunwa muke ji."

Dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya iso wurin zanga-zanga

Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Omoleye Sowore ya isa wurin da ake gudanar da zanga-zanga a jihar Lagos.

A wani faifan bidiyo da The Guardian ta wallafa, an gano Sowore a wurin zanga-zangar inda mutane ke shewa da murna.

Sowore a makon da ya gabata ya sha alwashin jagorantar zanga-zanga inda ya ce bai tsoron zaman gidan yari.

Jami'an tsaro sun mamaye Eagles Square

Yanzu haka jami'an tsaro sun rufe hanyar da za ta kai masu shirin zanga-zanga a babban filin taro na Eagles Square da ke Abuja.

Masu ababen hawa da yan jarida sun gaza shiga yankin domin gudanar da ayyukansu.

Jaridar Punch ta wallafa cewa Eagles Square a makare ta ke da jami'an tsaro a ciki da wajen filin taron, duk da cewa masu zanga-zanga sun nuna sha'awar amfani da filin domin taronsu.

Masu zanga zanga sun bijirewa sabon taken Najeriya

Wasu matasa da ke zanga-zanga a jihar Lagos sun gudanar da tsohon taken Najeriya domin nuna rashin jin dadinsu da ƙasar.

The Guardian ta wallafa faifan bidiyon masu zanga-zangar inda suka bijirewa sabon taken Najeriya da aka dawo da shi.

Wanann na zuwa ne yayin da ake cigaba da gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu saboda halin kunci da ake ciki.

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.