Kaduna: An Zargi Sojoji da Sake Jefa Bama Bamai a Masallaci Aka Kashe Bayin Allah
- Mazauna kauyuka biyu a jihar Kaduna sun zargi jami'an sojojin saman Najeriya da kai masu hari a masallaci da kasuwa
- An yi zargin mutane 23 aka gano da su ka hada da manoma da yara bayan kurar harin ta lafa, lamarin da aojojin su ka musanta
- Mataimakin daraktan yada labaran rundunar, Gruf Kyaftin Kabiru Ali ya yi bayanin cewa an kai harre-haren kan yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Wasu daga cikin mazauna karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna sun yi zargin jiragen sojojin saman Najeriya sun jefa masu bama-bamai.
Sun ce an jefa bam din a kan wani masallaci da kasuwa, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 23 zuwa yanzu.
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa mazauna yankunan sun ce an kai harin ne a wani yanayi mai kama da wanda jami'an su ka kai kan mazauna Tudun Biri, inda mutane sama da 100 su ka rasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano gawarwaki a harin Kaduna
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa zuwa yanzu, an gano gawarwakin jama'a akalla 23, daga ciki har da manoma da kananan yara.
Mazauna Jika da Kolo a karamar hukumar Giwa da aka kai wa harin sun samu sabani kan ainihin adadin wanda su ka rasu a harin.
Harin Kaduna: Rundunar sojin sama ta wanke kanta
Rundunar sojin saman kasar nan ta yi martani kan zarginta da kai hari kan mazauna karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Mataimakin daraktan yada labaran rundunar, Gruf Kyaftin Kabiru Ali ya ce jami'ansu sun kai farmaki kan wurin ajiye makaman yan bindiga a yankin da ke da alaka da Dogo Gide.
Kaduna: Yan bindiga sun kashe dan takara
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu yan ta'adda da ba a san ko su waye ba sun hallaka dan takarar kansila a karamar hukumar Kauru a Kaduna, Raymonda Timothy da kaninsa, James Timothy.
Shugaban karamar hukumar Kauru a Kaduna da ya tabbatar da harin ya nemi daukin jami'an tsaro wajen gano wadanda su ka tafka mummunan aiki, da kare afkuwar haka a gaga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng