Bello Turji: Sheikh Pantami Ya Fadi Dalilin Ƙaruwar Ta'addanci duk da Rajistar NIN

Bello Turji: Sheikh Pantami Ya Fadi Dalilin Ƙaruwar Ta'addanci duk da Rajistar NIN

  • Tsohon Ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Pantami ya fadi dalilin ƙaruwar ta'addanci da garkuwa da mutane
  • Pantami ya bayyana yadda ya yi nasarar hada layukan miliyoyin yan Najeriya da lambar NIN lokacin da ya ke ofis
  • Sai dai ya ce komai ya lalace bayan barinsa ofishin da kuma sauye-sauye da aka samu a sabuwar gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi magana kan ƙaruwar ta'addanci.

Farfesa Pantami ya yi ƙarin haske kan dalilin ƙaruwar garkuwa da mutane duk da kokarin hada layuka da lambar NIN.

Farfesa Pantami ya yi karin haske kan ƙaruwar ta'addanci a Najeriya
Farfesa Isa Ali Pantami ya fadi dalilin ƙaruwar ta'addanci a Najeriya. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Asali: Twitter

Ta'addanci: Pantami ya fadi dalilin ƙaruwar matsalar

Kara karanta wannan

Arewa na cikin matsala, ambaliya ta ƙara kashe mutum 29, gidaje 321,000 sun lalace

Tsohon Ministan ya fadi haka ne yayin amsa tambayoyi a jihar Katsina kan ƙaruwar ta'addanci, cewar rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Pantami ya ce barinsa ofis da kuma sauye-sauye a gwamnati sun taka rawa wurin lalacewar shirinsa.

Shehin malamin ya ce da kansa ya yi yunkurin samar da tsarin domin dakile ayyukan ta'addanci lokacin yana cikin gwamnati.

Ya ce an yi nasarar hada miliyoyin layukan yan Najeriya da NIN amma komai ya lalace bayan barinsa ofishin Minista a gwamnatin Buhari.

"Mun yi nasarar hada layukan yan Najeriya kusan miliyan 100 wanda ka'ida ne a dokar NIMC sashe na 26."
"Ya zama wajibi hada layukan ko da kuwa babu rashin tsaro, muhimmancinsa ya zarce tsaro har zuwa harkokin ilimi da lafiya da sauran abubuwa na cigaba."
"Hakan zai ba da damar gano bayanan mutum musamman lokacin da masu garkuwa suka sace mutane."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami’an gidan yari 4, ta fadi dalili

- Farfesa Isa Ali Pantami

Pantami ya fadi hanyar dakile ta'addanci

Sheikh Pantami ya ce duk da masu garkuwa da lambar wanda aka sace suke magana, dalilin haka sai dai a gano bayanan wanda aka sace.

Sai dai ya ce duk da haka babu wani kira a kasar da ba za a iya bibiyarsa ba tare da gano inda ake kiran.

Pantami ya yi magana kan 'mining'

Kun ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya yi magana kan 'mining' da kuma 'kirifto' inda ya shawarci malamai su yi taka tsan-tsan.

Farfesa Pantami ya ce bai kamata malamai suna gaggawar haramta abin da ba su da cikakken ilimi a kai ba.

Shehin malamin ya ce gagawar haramta abubuwa ke mayar da duniyar Musulunci baya a bangaren fasaha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.