'Yan Sanda Sun Damke Gungun 'Yan Fashin da Suka Addabi Al'umma

'Yan Sanda Sun Damke Gungun 'Yan Fashin da Suka Addabi Al'umma

  • Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta yi nasarar cafke wani gungun yan fashi da suka addabi mutane a karamar hukumar Misau
  • Ana zargin cewa yan fashin sun shiga wani gida da bindiga suka kwace makudan kudi da kayayyaki masu muhimmanci
  • Bayan binciken yan sanda, yan fashi da makamin sun amince da cewa sun aikata laifin tare da faɗin sauran da suke fashi tare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Rundunar yan sandan Najeriya ta yi nasarar cafke wasu da ake zargi da fashi da makami.

Rahotanni sun nuna cewa matasan sun fitini al'umma da sace-sace ne a karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun aika 'yan ta'adda 8 lahira, an ceto wanda aka yi garkuwa da su

Bauchi
An kama yan fashi a Bauchi. Hoto: Nigerian Police Force Bauchi State Command
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da rundunar yan sanda a Bauchi ta wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan fashi sun kai hari a kauyen Bauchi

Rundunar yan sanda ta zargi yan fashi da makamin da kai hari gidan wani mutum mai suna Malumi a ƙaramar hukumar Misau.

Ana zargin cewa sun shiga gidan da bindiga suka kwace kudi N250,000, wayoyin hannu guda uku da katin waya mai dimbin yawa.

An kama yan fashi da makami a Bauchi

Bayan tsananta bincike, rundunar yan sanda ta kama uku daga cikin yan fashin da suka kai hari gidan mutumin guda hudu kuma sun tsere.

Yan sanda sun kama su dauke da bindiga ƙirar Pistol da kuma harsashi guda bakwai da suke amfani wajen ta'addanci.

Maganar kwamishinan yan sanda

Kwamishinan yan sanda a jihar Bauchi, Auwal Musa Muhammad ya yi kira ga al'ummar jihar kan su cigaba da ba yan sanda hadin kai wajen gano barna.

Kara karanta wannan

An cafke dan ta'adda mai nuna bindiga a intanet da gungun yan fashi a Arewa

CP Auwal Musa Muhammad ya tabbatar da cewa za a mika waɗanda ake zargi da fashin gaban alkali da zarar an kammala bincike.

An kama yan fashi a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya a jihar Katsina ta yi nasarar cafke gungun yan ta'addan da suka addabi al'umma.

An ruwaito cewa yan ta'addar suna fashi da makami a kan hanya inda suke tare mutane suna kwace musu kudi da kayayyaki masu muhimmanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng