Dubi hotunan 'yan fashi da makami 48 da aka kama tare da makamai a Jihar Neja
Hukumar Yan sandan Najeriya tayi nasarar kama wasu mutane 48 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu da kuma satar motoccin al'umma a jihohin Neja, Kaduna, Filato, Katsina, Nasarawa, Zamfara da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Har ila yau, Yan sandan sunyi nasarar cafke wasu kungiyar bata gari wanda suka kware wajen kera bindigogi da harsashi don siyarwa ga yan fashi da sauran batagari cikin al'umma.
A sanarwan da mai magana da yawun Hukumar Yan sandan, CSP Jimoh Moshood ya bayar ta shafin Facebook na Hukumar, ya lissafo sunayen wandanda ake zargi da kuma muggan makamai, harasashi, kayayakin sadarwa, motocci, kudaden jabu da wasu ababen da aka same su dashi.
KU KARANTA: An kafa dokar hana fita a Mambilla bayan wani sabon rikici ya barke
Moshood ya yi kira ga al'umma da aka sace wa motocci su garzaya ofishin hukumar na jihar Neja tare da shaidar malakar motar da sauran takardu don su karbi motocin su.
Wadanda ake zargi din sun amsa laifin su kuma za'a gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kammala bincike.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng