An Damƙe Masu Garkuwa Da Ƴan Fashi Da Makami 23 a Filato

An Damƙe Masu Garkuwa Da Ƴan Fashi Da Makami 23 a Filato

- Rundunar sojojin Nigeriya ta ce dakarunta na Operation Safe Haven ta yi nasarar kama ɓata gari 23

- Wadanda aka kama sun hada da wadanda ake zargi da fashi da makami, garkuwa da mutane da mallakar bindigu

- Manjo Janar Dominic Onyemelu, kwamandan rundunar ne ya yi holen su a ranar Alhamis ya ce za a gurfanar da su

Dakarun sojoji, ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Safe Haven (OPSH) da ke aikin samar da zaman lafiya a sassan johohin Kaduna, Filato da Bauchi ta kama mutum 24 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mallakar bindigu ba bisa ka'ida ba da wasu laifukan.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Dominic Onyemelu ne ya gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a ranar Alhamis a Jos, Daily Trust ta ruwaito.

An Damƙe Masu Garkuwa Da Ƴan Fashi Da Makami 23 a Filato
An Damƙe Masu Garkuwa Da Ƴan Fashi Da Makami 23 a Filato. Hoto: @MobilePunch

DUBA WANNAN: NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano

Onyemelu ya ce rundunar ta samu wannan nasarorin ne saboda ƙara jajircewa da ta yi wurin gudanar da ayyukan ta.

Ya yi bayanin cewa 17 cikin waɗanda ake zargin suna da hannu a garkuwa da mutane ne, yayin da sauran gudun kuma fashi da makami da mallakar bindigu ba bisa ka'ida ba.

"Dakarun tsaro da hadin gwiwar ƴan banga da mutanen gari sun daƙile yunkurin hari suka kama mutum 17 da ake zargi.

"Mutane 17 ɗin da aka kama da babura 7, bindiga da aka ƙera a gida Nigeria, harsashi 2, adduna 13, ƙananan wuka 3, wayoyin salula 15 da layyu sun fito ne daga johohin Kaduna, Bauchi, Filato da Kano," a cewar kwamandan cikin jawabinsa.

KU KARANTA: Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

Ya ce an yi bincike kan wadanda ake zargin kuma za a gurfanar da su nan bada dadewa ba.

Ya yi kira ga mutane su cigaba da bawa rundunar haɗin kai da goyon baya don ganin ta samu nasara.

A wani labarin daban, rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.

Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164