An Shiga Sabon Makoki a Borno: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Halaka Mutane 4

An Shiga Sabon Makoki a Borno: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Halaka Mutane 4

  • Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta sanar da cewa hatsarin kwale-kwale ya yi sanadiyar mutuwar mata hudu a garin Dikwa
  • A cikin wata sanarwa daga kakakinta, ASP Nahum Daso, rundunar ta ce hatsarin ya faru ne a ranar Litinin a yankin Bakassi
  • Daga cikin wadanda suka mutu akwai dattijuwa da kuma jaririya 'yar wata biyar yayin da kuma aka mika gawarsu ga iyalansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Rahotanni sun bayyana cewa wani hatsarin kwale-kwale ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu a garin Dikwa da ke jihar Borno.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso ya sanar da cewa sun samu rahoton iftila'in ne a hedikwatar ‘yan sandan Dikwa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun aika 'yan ta'adda 8 lahira, an ceto wanda aka yi garkuwa da su

Rundunar 'yan sandan Borno ta yi magana kan hatsarin jirgin ruwa da ya halaka mata 4
Borno: Hatsarin kwale kwale ya halaka mata 4, 'yan sanda sun yi bayani. Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

Kwale kwale ya yi hatsari a Borno

Tashar Channels TV ta ruwaito ASP Nahum Daso ya ce rundunar ta samu rahoton cewa wani mummunan hatsarin kwale-kwale ya afku a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in rundunar ya ce hatsarin jirgin ruwan ya faru a yankin Bakassi, tsakanin Mafa da Dikwa kan hanyar Maiduguri, jihar Borno.

Sanarwar 'yan sandan ta ce hatsarin ya rutsa da kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji inda ya nutse a cikin ruwa, wanda hakan ya yi sanadin rasa rayukan mata hudu.

Hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar matan hudu da suka fito daga unguwar Bulabulin da ke Dikwa.

Mata 4 sun mutu a hatsarin Borno

Wadanda suka mutu a hatsarin sun hada da Ya Mallum Shettima, wata babbar mace ‘yar karamar hukumar Marte da Maimuna Akura ‘yar shekara 10.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Ana tsaka da kada kuri'a, 'yan bindiga sun yi awon gaba da akwatin zabe

Sauran matan su ne: Umira Alhaji Bulama ‘yar shekara 6, sai kuma Yagana Bulama Kawu mai wata biyar da haihuwa.

Ba tare da bata lokaci ba aka kwashe matan zuwa babban asibitin Dikwa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu inji rahoton jaridar Vanguad.

Bayan haka, an mika gawarwakin ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Mawakiyar addini ta kwanta dama

A wani labarin, mun ruwaito cewa shahararriyar mawakin begen Annabi da harshen Yarbanci, Rukayat Gawat ta rigamu gidan gaskiya.

Malamin addinin Musulunci na garin Ilorin da ke jihar Kwara, Alfa Aribidesi At-Tawdeeh ya sanar da rasuwar mawakiyar a ranar 24 ga Satumba, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.