Hatsarin kwale-kwale ya halaka rayuka 15 a Bauchi - NEMA

Hatsarin kwale-kwale ya halaka rayuka 15 a Bauchi - NEMA

Babban sakataren hukumar kula da al'amuran gaggawa na jihar Bauchi, SEMA, Shehu Ningi, a ranar Alhamis ya ce kusan mutum 15 suka rasu sakamakon nitsewar da kwale-kwale tayi a kauyen Gwaskaram da ke karamar hukumar Bauchi ta jihar.

Ningi ya tabbatar da aukuwar lamarin ne a wata tattaunawa da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Bauchi.

Ya ce kwale-kwalen na dauke da fasinjoji daga kauyen Gwaskaram inda suka nufi kauyen Yola Doka don cin kasuwa.

Ningi ya ce lamarin ya faru ne a cikin kwanakin karshen mako a rafin Gwaskaram da ke karamar hukumar Bauchi ta jihar.

Ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 15 yayin da aka ceto mutum uku duk da dai har yanzu ana ci gaba da neman sauran.

Babban sakataren SEMA ya tabbatar cewa ana ci gaba da neman sauran gawawwakin a cikin rafin, jaridar Daily Nigerian ta tabbatar.

Hatsarin kwale-kwale ya halaka rayuka 15 a Bauchi - NEMA
Hatsarin kwale-kwale ya halaka rayuka 15 a Bauchi - NEMA. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna)

Ningi ya ce kwale-kwalen ta nitse ne sakamakon cika jama'a da aka yi da kuma rashin gyara. Wani rami ne gareta inda ruwa ya dinga shiga har ta nitse.

Ya ce kwale-kwalen na dauke da mutane 21 ne kuma ko daga gani an san ta yi musu kadan.

Dagacin kauyen Gwaskaram, Abdullahi Maikano, ya sanar da NAN a tattaunawar waya, cewa kwale-kwalen na dauke da sama da mutum 20 lokacin da ta nitse.

"An ceto biyar daga ciki kuma gawawwakin mutum biyar aka samu a halin yanzu," yace.

Ya kara da cewa tuni aka bazama neman gawawwakin a rafin.

Ya yi kira ga iyalan mamatan da su dubi abinda ya faru a matsayin kaddara daga Allah kuma su jure tare da imani.

A wani labari na daban, kamar yadda rahotanni daga jihar Sokoto suka bayyana, an kashe mutum kusan 60 a cikin wasu hare-haren da 'yan bindiga suka kai a ranar Laraba, 27 ga watan Mayun 2020 a wasu kauyuka na karamar hukumar Sabon-Birnin-Gobir.

Ganau ba jiyau ba, sun ce maharan sun dauki tsawon sa'o'i suna ruwan wuta a kauyukan ba tare da kowa ya tunkaresu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: