Katsina: Bayan Kisan Sabubu, an Hallaka Kanin Dan Ta'adda da Ya Addabi Jama'a

Katsina: Bayan Kisan Sabubu, an Hallaka Kanin Dan Ta'adda da Ya Addabi Jama'a

  • Kasa da mako daya bayan kisan Halilu Sabubu, rundunar yan sanda ta yi nasarar hallaka wani dan bindiga
  • Jami'an tsaron sun yi nasarar hallaka Dan Kundu wanda kani ne ga dan ta'adda, Usman Modi Modi
  • An yi nasarar hallaka Dan Kundu ne a wani arangama da jam'an tsaron yayin da suke shirin kai hari a yankin Kurfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Rundunar yan sanda ta sake hallaka wani rikakken dan ta'adda a jihar Katsina, Dan Kundu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Dan Kundu kani ne ga kasurgumin dan bindiga, Usman Modi Modi.

Yan sanda sun hallaka rikakken dan ta'adda, Dan Kundu
Rundunar yan sanda sun hallaka kasurgumin dan ta'adda, Dan Kundu a Katsina. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Katsina: Yan sanda sun hallaka dan bindiga

Zagazola Makama ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.

Kara karanta wannan

An cafke dan ta'adda mai nuna bindiga a intanet da gungun yan fashi a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da cewa Dan Kundu ya yi suna wurin addabar yankin karamar hukumar Safana a dajin Tsatskiya.

An yi nasarar hallaka Dan Kundu ne yayin arangama da jami'an yan sanda da kuma taimakon yan banga.

Kisan Dan Kundu ya faru ne a daren ranar Alhamis 19 ga watan Satumbar 2024 a kokarin kai hari a yankin Kurfi.

Jami'an tsaron sun yi nasarar dakile harin da suka yi niyyar kawowa da yaransa inda aka hallaka da dama.

Yadda aka hallaka Halilu Sabubu a Zamfara

Wannan na zuwa ne bayan kisan rikakken dan ta'adda, Haliliu Sabubu a ranar Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024.

Kisan Sabubu ya yi wa yan Najeriya da dama dadi duba da yadda dan ta'addan ya addabi al'umma musamman a yankin Arewa maso Yamma.

"Bello Turji ya tsorata" - Sheikh Asada

Kara karanta wannan

Yunwa na neman kashe shi a Katsina, Kwankwaso ya ceci ran karamin yaro

Kun ji cewa Sheikh Murtala Bello Asada ya sake kalubalantar Bello Turji a wani bidiyo inda ya tabbatar da zargin ana daukar nauyin ta'addanci.

Malamin ya ce Turji a faifan bidiyo, ya tabbatar da hannun karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle wajen harkar ta'addanci.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kisan rikakken dan ta'adda, Halilu Sabubu a Zamfara a ranar Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.