Abin da Abdulaziz Yar’adua Ya Fadawa Kwankwaso Lokacin Ta’aziyyar Dada a Katsina

Abin da Abdulaziz Yar’adua Ya Fadawa Kwankwaso Lokacin Ta’aziyyar Dada a Katsina

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya na cikin wadanda su ka je yin ta’aziyya da Hajiya Dada Yar’adua ta rasu
  • ‘Dan takaran shugaban kasar a zaben 2023 ya na da tsohuwar alaka da gidan Yar’adua tun a shekarun 1990s
  • Abdulaziz Musa Yar’adua ya tuna da dangantakar Kwankwaso da Shehu Yar’adua tun People Front zuwa SDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Katsina - Kwanakin baya Katsina ta cika saboda rasuwar Hajiya Dada Yar’adua wanda ita ce mahaifiyar Umaru Musa Yar’adua.

Kusan duk wani babba a kasar nan ya ziyarci Katsina domin yi wa dangin tsohon shugaban Najeriyan da mutanen jihar ta’aziyya.

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a gidan Yar'adua a jihar Katsina Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Rabiu Kwankwaso ya je ta'aziyyar Dada Yar'adua

Legit Hausa ta lura Rabiu Musa Kwankwaso bai samu sallar jana’izar ba amma yana daga cikin wadanda suka je ta’aziyya daga baya.

Kara karanta wannan

"Za mu ceto ku": Kwankwaso ya fadi niyyarsa game da mulki a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda hotuna suka fito daga shafinsa dandalin X, Kwankwaso ya je Katsina da mutanensa kuma ya hadu da wasu 'yan siyasa.

A cikin tawagarsa akwai 'yan Kwankwasiyya da shugabannin jam’iyyar NNPP na Katsina da suka yi masa rakiya zuwa Yar’adua.

Abdulaziz Yar’adua ya fada kan Kwankwaso

Da ya tashi yin jawabi, daya daga cikin manyan dangin a yau, Abdulaziz Musa Yar’adua ya yi maganar alakarsu da Kwankwaso.

Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua ya ce sun tashi ne sun ga ‘dan siyasar a gidansu domin dangantakarsa da Shehu Musa Yar’adua.

Bayan nan kuma Kwankwaso da Ummaru Yar’adua sun kasance gwamnoni a lokaci guda lokacin da PDP ta kafa gwamnati a 1999.

Sanatan na Katsina ta tsakiya ya yabawa irin fadi-tashin da jagoran na Kwankwasiyya yake yi domin a tallafawa talaka.

Sannan kuma ya godewa shawarwarin da ya ce Sanata Kwankwaso su na ba kamarsa wadanda suke yi wa kallon kannensu a yau.

Kara karanta wannan

Yunwa na neman kashe shi a Katsina, Kwankwaso ya ceci ran karamin yaro

Gidan Yar'adua da mutanen Kano

‘Dan majalisar ya kuma tabbatar da kyakkyawar alakar da ke tsakanin gidan Yar’adua da Kano ya na misali da Abba Kabir Yusuf.

Bayan gwamna Abba Kabir Yusuf da ya zo ta’ziyya, Mai martaba Sarkin Kano watau Muhammadu Sanusi II ya zo Katsina da rasuwar.

Kwankwaso ya tuna da Dada Yar'adua

Da ya tashi jawabi, Kwankwaso ya fadi gudumuwar da Shehu Yar’adua ya ba shi ya zama mataimakin shugaban majalisa a 1992.

Tsohon gwamnan ya tuna alakarsa da gidan tare da addu’a ga Ubangiji SWT ya ji kan Dada da ya kira da uwa kuma kaka ga al'umma.

Dangote, Atiku da Kwankwaso sun je Borno

Kun ji labari cewa mutanen Borno sun samu tallafin N3bn a sanadiyyar Alhaji Aminu Dantata da Aminu Aliko Dangote da wasunsu.

Masu kudi da 'yan siyasa irinsu Alhaji Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso sun ba da tallafi da ambaliya ta rutsa da su a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng