Malamin Musulunci Ya yi Bayani kan Karbar Tuban Bello Turji da sauran Yan Bindiga

Malamin Musulunci Ya yi Bayani kan Karbar Tuban Bello Turji da sauran Yan Bindiga

  • Sojojin Najeriya sun cigaba da samun nasara a kan yan bindiga musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Wani Malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Adam Muhammad Albani ya yi bayani kan tuban yan ta'adda
  • Masu sauraron Sheikh Albanin Gombe sun nuna shakku kan hukuncin da ya fada na karɓar tuban Turji da ya fitini jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Wani malamin addinin Musulunci a Gombe ya yi bayani kan karɓar tuban yan ta'adda irinsu Bello Turji.

Sheikh Adam Muhammad Albani ya ce matuƙar yan ta'adda suka ajiye makamai da gaske za a karbi tubansu a addini.

Albani Gombe
Malami ya yi bayani kan tuban Bello Turji. Hoto: Sheikh Adam Muhammad Albani Gombe
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Sheikh Adam Muhammad Albani ya yi ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

"Baban Bello Turji mutumin kirki ne": Malamin Musulunci ya fadi halin dattijo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kisan manyan yan ta'adda a Arewa

A kwanan nan sojojin Najeriya na cigaba da samun nasara kan manyan yan bindiga a Arewa wanda wasu ke ganin ya kamata su fara tuba.

Legit ta ruwaito cewa ko a makon da ya wuce sojojin Najeriya sun hallaka babban dan bindiga, Halilu Sabubu a jihar Zamfara.

Za a karbi tuban Bello Turji a Musulunci?

Sheikh Adam Muhammad Albani ya fadi hukuncin Musulunci idan Bello Turji a ajiye makamai da kansa ya zo da mabiyansa ya nemi gafara.

Malamin ya ce idan ya aikata haka, Shari'a za ta karbi tubansa kuma ba za a kashe shi ba matuƙar da gaske yake ya tuba.

Dalibai sun yi shakkar tuban Bello Turji

Sai dai a bidiyon, bayan malamin ya gama bayani masu sauraronsa sun nuna shakku kan yarda da karɓar tuban dan ta'addar.

Kara karanta wannan

"Turji ya tsorata": Malamin Musulunci ya dira kan dan ta'adda, ya kalubanci Matawalle

Amma malamin ya ce aya ya karanto musu, ya kuma kara da cewa idan ba su yarda ba sai su kawo ayar da ta nuna ba haka ba ne.

An kai sojoji garin Moriki saboda Turji

A wani rahoton, kun ki cewa mutanen garin Moriki a ƙaramar hukumar Shinkafi sun fara zaman ɗar-ɗar bayan sun kasa biyan Bello Turji N30m.

Yayin da wa'adin da ƙasurgumim ɗan bindigar ya bayar ke cika, an ƙara girke dakarun sojoji da askarawan Zamfara a garin Moriki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng