'Gwamna Ya ba da Umarnin Cire Allunan Tallar Tinubu a Jiharsa,' APC Ta Dauki Zafi

'Gwamna Ya ba da Umarnin Cire Allunan Tallar Tinubu a Jiharsa,' APC Ta Dauki Zafi

  • Jam'iyyar APC ta ce ta gano wani shirin gwamnatin Anambra na cire dukkanin allunan tallar Shugaba Bola Tinubu a fadin jihar
  • APC ta ce hukumar tallace tallace ta jihar ce ta sanar da ita cewa umarnin cire allunan ya fito daga sama, lamarin da ya sa ta yi magana
  • Amma da aka tuntubi kwamishinan yada labarai na jihar, Dakta Law Mefor, ya ce ba allunan Tinubu ne aka ba da umarnin cirewa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra: Jam’iyyar APC ta bayyana damuwarta kan umarnin gwamnan Anambra, Charles Soludo na cire allunan shugaban kasa Bola Tinubu daga jihar.

An ce Sir Paul Chukwuma, fitaccen dan takara a zaben gwamnan Anambra na 2025 ne ya sanya allunan a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.

Kara karanta wannan

PDP ta gaji da lamarin gwamnan Sokoto, ta bukaci EFCC ta binciki N30bn da ya ware

Jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin Anambra da cire allunan tallar Tinubu a jihar
Jam'iyyar APC ta ce gwamnan Anambra ya ba da umarnin cire allunan Tinubu a jiharsa. Hoto: AFP
Asali: AFP

Cire allunan Tinubu: APC ta dauki zafi

Jam'iyyar APC ta ce ta tuntubi hukumar tallace tallace ta Anambra kan lamarin, inda ta samu bayanin cewa umarnin cire allunan ya fito ne daga sama, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce ofishin yakin neman zaben Sir Paul Chukwuma ya tuntubi shugabannin APC na Kudu maso Gabashin kasar ciki har da gwamnan Imo, Cif Hope Uzodinma kan lamarin.

Jam'iyyar APC ta caccaki gwamnatin jam'iyyar APGA mai mulki a jihar kan ba da umarnin cire allunan, inda ta zarge ta da gaza magance kashe kashen da ake yi a jihar.

Maimakon magance matsalolin da suka addabi jihar, APC ta ce gwamnatin APGA a jihar ta mayar da hankali wajen yi wa jam'iyyun adawa bi-ta-da-kulli.

Gwamnati ta karyata zargin jamiyyar APC

Da aka tuntubi kwamishinan yada labarai na jihar, Dakta Law Mefor, ya ce gwamnati ba ta cire allunan tallan shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

Olumide Akpata: Dan takarar LP mai barazana ga jam'iyyu a zaben Edo

Dakta Law Mefor ya ce gwamnatin jihar ta dai sa a cire allunan yakin neman zabe na wani dan takara amma ba na Tinubu ba.

"Shin ba mu san dokokin da aka kafa ba ne? Akwai lokacin gudanar da komai, kuma lokacin fara yakin neman zabe bai yi ba.
Baya ga haka, ai shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ba neman takarar gwamna a jihar Anambra ya ke yi ba, don me za a cire allunansa?"

An gurfanar da shugaban NURTW

A wani labarin, mun ruwaito cewa an gurfanar da Mukaila Lamidi, da aka fi sani da Auxilliary, shugaban kungiyar NURTW na Oyo a kotu kan lalata allunan tallar Bola Tinubu,.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ne aka ce ya gufarnar da shugaban kungiyar direbobin kan tuhume-tuhumen da suka hada da barnata dukiyar jam'iyyar APC da gangan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.