Mai gadi ya shiga halin ha-ula'i bayan da aka kamashi yana cire allunan tallar APC

Mai gadi ya shiga halin ha-ula'i bayan da aka kamashi yana cire allunan tallar APC

- Wata kotun majistire da ke a Minna, jihar Niger ta garkame wani mai gadi tsawon watanni 3, bisa laifin cire allunan tallar jam'iyyar APC a garin Minna

- Bayan da aka gabatar da tuhumar a gaban kotu, wanda ake karar, ya amsa laifinsa, tare da rokon kotu da ta sassauta masa

Rahotanni sun bayyana cewa wata kotun majistire da ke a Minna, jihar Niger ta garkame wani mai gadi a gidan kaso na watanni 3, sakamakon kama shi da laifin cire allunan tallar jam'iyyar APC a garin Minna.

Isiyaka mai shekaru 35, an kama shi da laifin rashin gaskiya, wanda ya ke a cikin sashi na 327 na dokar shari'a.

Jami'in hukumar tsaro ta yan sanda da ya shigar da karar kotu, Sifeta Ahmed Ali, ya sanar da kotun cewa an cafke Isyaku a ranar 8 ga watan Satumbar wannan shekarar, bayan da aka same shi yana cire allunan tallar APC.

KARANTA WANNAN: Rikici ya kunno kai a Jam'iyyar PDP sakamakon wani sabon hukunci da ta yanke

Kotu ta garkame mai gadi bayan da aka kamashi yana cire allunan tallar APC
Kotu ta garkame mai gadi bayan da aka kamashi yana cire allunan tallar APC
Asali: Facebook

Ali ya ce mai laifin, wanda ke da zama a yankin Chanchaga, bayan da kwamitin tsaro na Chanchaga suka kama shi, sun mika shi ga wani shugaban jam'iyyar ta APC a yankin, SalihuAdamu, wanda shi kuma ya mikashi ga yan sanda.

Mai karar ya ce a lokacin da ake tuhumar Isiyaku, sai cewa yayi yaga wasu da ba asan ko suwa ye ba sun cire allunan tallar PDP na yankin, don haka ya yanke shawarar cire na APC da ke a kan hanyar ta Minna zuwa Suleja.

Bayan da aka gabatar da tuhumar a gaban kotu, wanda ake karar, ya amsa laifinsa, tare da rokon kotu da ta sassauta masa.

Sai dai wanda ya shigar da karar, ya roki kotu da ta hukunta shi bisa sashi na 157 ada ke a cikin dokar shari'ar ta'addanci.

Mai shari'a, Sa'adatu Gambo, ta baiwa Isyaku umurnin biyan tarar 10,000 ko kuma ya kwashe watanni 3 a gidan kaso, ma damar ya gaza biyan kudin tarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel