Zaben 2023: Magoya baya sun fara baza fastocin takarar Bola Tinubu a lungunan Legas

Zaben 2023: Magoya baya sun fara baza fastocin takarar Bola Tinubu a lungunan Legas

  • Hotunan neman takarar Asiwaju Bola Tinubu suna yawo a unguwannin Legas
  • Magoya bayan Bola Tinubu suna baza fastocin 2023 a Ojota, Maryland, da Ikeja
  • Bayan haka an ga wasu hotunan Tinubu a yankunan Ikorodu, Ikotun da Igando

Lagos - Duk da cewa babban jigon jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, bai bayyana niyyar shiga takara ba, wasu na ta yi masa yakin zabe.

Jaridar Punch ta kawo rahoto cewa hotunan Asiwaju Bola Tinubu yana neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 sun fara zagaye garin Legas.

Rahotanni sun ce an ga fastocin tsohon gwamnan na jihar Legas a wasu unguwannin Legas kamar su Ojota, Maryland, Ketu Ikeja, da kuma Lagos Island.

Haka zalika an baza hotunan Tinubu a Ikorodu, Ikotun, Igando, da unguwar Ojuelegba, da sauransu.

Read also

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Sai dai magoya bayan ‘dan siyasar da suka buga wadannan hotunan kamfe, ba su bayyana wanda ake sa rai zai yi wa Tinubu abokin takara a zaben na 2023 ba.

Bola Ahmed-Tinubu
Asiwaju Bola Ahmed-Tinubu Hoto: www.adabanijaglobal.com.ng
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar SWAGA’23 ta dage da kamfe

Bayan haka, kungiyar da tayi fice wajen yi masa kamfe, Southwest Agenda for Asiwaju, SWAGA’23 ta dage wajen wayar da kan mutane kan takararsa a Kudu.

Prince Dayo Adeyeye wanda ya yi aiki da Marigayi Moshood Abiola shi ne ya kafa wannan kungiya ta SWAGA domin ganin Bola Tinubu ya karbi mulki.

Jaridar tace Prince Adeyeye ya kaddamar da ofisoshin kamfe a Osun, Ogun, Ondo da Ekiti. Tun a karshen shekarar 2015 aka bude babban ofis a garin Ibadan.

Sarakuna suna tare da Tinubu a 2023

Irin wannan yunkuri ya sa Southwest Agenda for Asiwaju ta gana da sarakunan Legas a jiya.

Read also

Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023

Sarakunan da suka yi wa Tinubu mubaya’a a zaman da aka yi sun hada da Onigando na Igando, Oba Lasisi Gbadamosi, Ojora na kasar Ijora, Sarki Fatai Ojora.

Ragowar Sarakunan sune Oniru na Iruland, Oba Gbolahan Lawal, da Elegushi na kasar Ikateland.

Doyin Okupe zai nemi tikitin PDP

A makon nan ne aka ji cewa tsohon Mai magana da yawun Shugaban Najeriya, Doyin Okupe, zai tsaya takara a zaben 2023 domin ya shawo kan matsalar kasar.

Doyin Okupe yace Talaka zai ji dadi idan ya yi mulki, ya yi alkawarin samar da 30000MW na karfin wutar lantarki domin a fitar da talaka daga cikin duhu.

Source: Legit

Online view pixel