“Baban Bello Turji Mutumin Kirki ne”: Malamin Musulunci Ya Fadi Halin Dattijo

“Baban Bello Turji Mutumin Kirki ne”: Malamin Musulunci Ya Fadi Halin Dattijo

  • Fitaccen malamin Musulunci, Malam Murtala Bello Asada ya fadi halayen mahaifin dan ta'adda, Bello Turji
  • Shehin ya ce mahafin dan ta'addan, Usman Mani mutumin kirki ne wanda halayen dan nasa ya tilasta masa kaura
  • Sheikh Murtala Asada ya kuma kalubalanci karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle kan zargin hannu a ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Sheikh Murtala Bello Asada ya sake magana kan kasurgumin dan ta'adda Bello Turji da ake nema.

Shehin malamin ya ce hatta mahaifin Bello Turji da ake kira Usman Mani sai da ya bar gari inda ya wuce Kano.

Malam Musulunci, Bello Asada ya fadi halin mahaifin Bello Turji
Sheikh Murtala Bello Asada ya kalubalanci masu daukar nauyin ta'addanci bayan bidiyon Bello Turji. Hoto: Malam Murtala Bello Asada.
Asali: Facebook

Sheikh Asada ya magantu kan mahaifin Turji

Kara karanta wannan

"Turji ya tsorata": Malamin Musulunci ya dira kan dan ta'adda, ya kalubanci Matawalle

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da hadimin gwamnan Zamfara, Mugira Yusuf ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Murtala Bello ya ce jami'an tsaro sun taba kama mahaifin Turji inda dan ta'addan ya ba da wa'adin awanni shida a sako masa mahaifinsa.

Shehi ya ce Turji ya yi barazanar tona asirin Turuzzan birni a harkar ta'addanci kafin wani lokaci an dauko mahaifinsa a mota kirar Hilux.

"Baban Bello Turji da ake kira Usman Mani mutumin kirki ne, bakin cikin dansa ya saka shi komawa Kano wani wuri da ake kira Kura ya zauna."
"Da can ma bakin ciki ya ishe shi ya koma Jigawa yana harkokinsa, daga nan jam'ian tsaro suka cafke shi da cewa Turji yana tura masa shanu."
"Da Turji ya ga haka ya ba da sanarwa cewa a dawo da mahaifinsa cikin awanni shida ko ya tonawa Turuzzan birnin asiri, wa ya ba uban Turji Hilux aka dawo da shi? ku tambayar mana shi."

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi lokacin gamawa da Turji, ya tona abin da ke rura wutar

- Murtala Bello Asada

Turji: Sheikh Asada ya roki sojoji alfarma

Murtala Bello Asada ya ce yana da tabbacin jami'an sojoji suna da kwarewar kawo karshensa sai dai idan ba a ga dama ba.

Malamin ya ce bai son a kashe Turji so yake a rike shi ya fadi masu daukar nauyin ta'addanci sannan shi kuma ya yi masa jawabi.

Bello Asada ya kalubalanci Bello Matawalle

Kun ji cewa Sheikh Murtala Bello Asada ya sake kalubalantar Bello Turji a wani bidiyo inda ya tabbatar da zargin ana daukar nauyin ta'addanci.

Malamin ya ce Turji a faifan bidiyo ya tabbatar da hannun karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle a harkar ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.