Bafarawa: Tsohon Gwamna Ya ba 'Yan Sokoto Tallafin N1bn Su Rage Radadin Talauci

Bafarawa: Tsohon Gwamna Ya ba 'Yan Sokoto Tallafin N1bn Su Rage Radadin Talauci

  • Bayan shekaru 17 da sauka daga mulki, Alhaji Attahiru Bafarawa ya yi wata babbar hobbasa domin taimakawa al'ummar jihar Sokoto
  • A cewar tsohon gwamnan, a yanzu ne lokacin da ya fi dacewa ya kai dauki ga mutanen Sokoto saboda tsadar rayuwa da ake fuskanta
  • Bafarawa ya sanar da ba 'yan Sokoto tallafin Naira biliyan daya domin su rage radadin talauci tare da bayyana yadda rabon zai kasance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa ya kai dauki ga al'ummar jiharsa yayin da kasar nan ke fuskantar matsin tattalin arziki.

Alhaji Attahiru Bafarawa ya ba al'ummar Sokoto tallafin zunzurutun kudi har Naira biliyan daya domin su rage radadin talaucin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Dattijon attajiri, Dantata ya tallafa wa Borno da sama da Naira biliyan 1

Attahiru Bafarawa ya yi magana kan tsadar rayuwa a jihar Sokoto
Attahiru Bafarawa ya ba da tallafin N1bn ga al'ummar Sokoto domin rage radadin rayuwa. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai da jaridar Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Attahiru Bafarawa ya ba Sokoto tallafin N1bn

An rahoto cewa tsohon gwamnan Sokoto ya ba da talallafin Naira biliyan guda ga jihar ne a wani taro da gidauniyar Attahiru Bafarawa ta shirya a ranar Talata.

A wajen taron, Bafarawa ya ce ya ba da tallafin kudin ne domin ya nuna godiya ga aminci da yardar da al'ummar jihar Sokoto suka nuna masa a shekaru takwas na mulkinsa.

Ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata ya waiwayi al'ummar jihar domin taimaka masu a yayin da kowa ya ke fafutukar shallake wannan yanayi na tsadar rayuwa.

A cewar tsohon gwamnan, duk da cewa ya bar mulki kimanin shekaru 17 da suka gabata, amma har yanzu bai manta da halaccin 'yan Sokoto ba, saboda haka dole ya taimaka masu.

Kara karanta wannan

'Ka da mu zargi kowa': Tinubu ya bayyana abin da ya jawo ambaliyar Maiduguri

Sakon Alhaji Bafarawa ga Sakkwatawa

This Day ta ce tsohon gwamnan na Sokoto ya jaddada cewa yanzu lokaci ne na waiwayar jama'a da rage masu radadin da suke fuskanta inda ya ce:

"Babu lokacin da mutane ke bukatar taimako kamar yanzu, saboda haka na yanke shawarar samar da zunzurutun kudi har Naira biliyan daya domin jin dadin al’ummar Sokoto.
“Na damka gudanar da wannan asusu ga kwamitin da na kafa. Kwamitin yana karkashin jagorancin Alhaji Lawal Maidoki (Sadaukin Sokoto) wanda aka san shi da amana.
“Na bayar da wannan gudumawa ga al’ummar jihar Sokoto domin cike gibin da na bari a lokacin da nake mulki. Ina rokon Allah ya yafe mun kura kuraina."

'Yan bindiga sun farmaki Bafarawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa.

An ruwaito cewa 'yan bindigar sun kai wa Bafarawa hari ne awanni bayan da ya kaddamar da wata gidauniya ta taimakawa wadanda hare-haren 'yan bindiga ya shafa a Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.