Tsohon gwamnan Sokoto Bafarawa ya ziyarci al'ummar Hausawa a Ile-Ife

Tsohon gwamnan Sokoto Bafarawa ya ziyarci al'ummar Hausawa a Ile-Ife

Sarki mafi daraja daga sarautar kasar Yarbawa a kudancin Najeriya, Ooni na Ife Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II ya baiyana tsohon gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa da kasancewa daya daga cikin muhimman dattawan da har yanzu Nijeriya take amfana da su dangane da dattako, fadin gaskiya da tsoron Allah a cikin lamuransu da tallafawa al'umma.

Hausawa a Ile-Ife
Hausawa a Ile-Ife

Legit.ng ta samu labarin cewa Sarkin Ooni na Ife, Adeyeye Onitan dake jihar Osun ya fadi haka a fadarsa ta Ife a lokacin da yake karbar tawaga ta mussaman da tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya tura garin Ife dangane da yi wa al'ummar Hausawa jaje da bayar da gudumuwa na kudi har naira miliyan goma ga al'ummar Hausawa wadanda bala'in rikicin kabilanci ya farwa a farkon watan jiya.

Sarkin Ife yace, ba shakka ya san tsohon gwamnan sosai kuma sun hadu a lokuta dabam dabam, amma zahiri bai ganin a Najeriya akwai irinsa da ya hada gaskiya, son jama'a da rashin tsoro wajen tabbatar da hakkin al'umma tare da tsoron Allah a wuri daya irinsa ba.

KU KARANTA: Wani babban dan Boko haram ya mika wuya

Tun da farko jagoran tawagar Alhaji Abubakar Saddik Sanyinna, tsohon kwamishinan Ayyukan Gona na jahar Sokoto ya baiyana ma Ooni na Ife dalilin zuwan tawagar a garin tare da yaba masa dangane da matakin da ya dauka ga nuna rashin jin dadinsa dangane da abin da ya faru tsakani al'ummar Hausawa da Yarbawa wajen tayar da rikicin.

Wasu daga cikin wakilan tawagar sun kunshi Alhaji Nasiru Bafarawa, Alhaji Yusuf Dingyadi, Alhaji Sani Kabir, Sarkin Hausawan Lagos, Hon. Awwal M Ahmed Asaba, Alhaji Danlami Ibadan da sauran shugabanin Hausawa mazauna kudancin Najeriya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda wasu yarbawa suka taimakawa Hausawa a lokacin rikicin ile ife

Asali: Legit.ng

Online view pixel