Bafarawa ya bayyana dalilin da yasa Buhari ya yi bakin jini wurin shugabannin arewa

Bafarawa ya bayyana dalilin da yasa Buhari ya yi bakin jini wurin shugabannin arewa

- Attahiru Dalhatu Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Sokoto, ya bayyana dalilin da yasa shugabannin arewa suka dawo daga rakiyar Buhari

- Kazalika, tsohon gwamnan ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari akan kashe makudan kudi domin sayen allurar rigakafin korona

- Bafarwa ya bayyana cewa matsalar Nigeria ta tsaro ce ba annobar cutar korona ba

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya bayyana cewa gazawar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta fuskar tsaro ta jawo masa bakin jini a wurin dattijan yankin arewa.

Bafarawa ya shugabanci jihar Sokoto daga shekarar 1999 zuwa 2007 a karkashin inuwar tsohuwar jam'iyyar ANPP.

Tsohon gwamnan ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari akan kashe makudan biliyoyi akan annobar korona yayin da aka bar harkar tsaro tana cigaba da lalacewa, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Bafarawa ya bayyana cewa har yanzu ba'a samu mutum 2,000 da annobar korona ta hallaka ba, amma akwai dubun dubatar mutanen da 'yan ta'adda suka kashe.

KARANTA: An gargadi gwamna Yahaya Bello akan sukar allurar rigakafin cutar korona

A cewar Bafarawa, ba zai yi wu shugabannin arewa su rufe bakinsu, su ki yin magana ba a yayin da ake cigaba da kashe musu al'umma.

Bafarawa ya bayyana dalilin da yasa Buhari ya yi bakin jini wurin shugabannin arewa
Bafarawa ya bayyana dalilin da yasa Buhari ya yi bakin jini wurin shugabannin arewa
Asali: Twitter

Dubban jama'a ne suka rasa rayukansu a yayin da aka raba miliyoyi da muhallinsu sakamakon kalubalen tsaro da yankin arewa ya shiga, a cewar Bafarawa.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

"Ba zai yiwu mu rufe bakinmu ba saboda shugaban kasa dan arewa ne. Idan bamu yi magana ba yanzu bai kamata mu yi magana ba idan hakan ta cigaba a karkashin shugaban kasa dan kudancin Nigeria.

"An raba dubban mutane da muhallinsu a arewa da sauran sassan Nigeria, amma a haka gwamnati ta ware miliyan N400 domin sayen rigakafin allurar rigakafin korona, me yasa ba za'a kashe kudaden wajen sayen kayan aikin tsaro ba? Rashin tsaro ne matsalar mu a Nigeria ba annobar korona ba.

"Ko sati ba'a yi ba sai da aka kashe mutane 14 a kauyena a Sokoto. Babu gaskiya a batun cewa ana samun cigaba a bangaren tabarbarewar tsaro.

"Lamura kara lalacewa suke yi. Idan ka ziyarci makarantu a arewa, zaka samu yara marayu da yawa, 'yan bindiga sun kashe iyayensu," a cewar Bafarawa.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kai ziyara jihar Sokoto don jajantawa takwaransa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, bisa mummunar gobarar kasuwar da ta faru ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Yayin ziyarar, gwamna Wike ya bawa gwamnatin jihar Sokoto gudunmuwar milyan dari biyar (N500,000,000) domin sake gina kasuwar.

Hakazalika, Wike ya kai ziyara fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubuakar Sa'ad.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel