SSCE: Matakai 5 da Dalibai Za Su Bi domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO 2024

SSCE: Matakai 5 da Dalibai Za Su Bi domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO 2024

  • Duka wadanda suka zana jarabawar NECO ta 2024 za su iya duba sakamakonsu ta hanyar ziyartar shafin hukumar na yanar gizo
  • Daliban da suka zana NECO kuma suke son duba sakamakonsu, za su yi amfani da lambar rajista, lambar sirri da shekarar jarrabawar
  • A cikin wannan labarin, Legit Hausa ta samar da matakai daki-daki na yadda dalibai za su iya duba sakamakon jarabawarsu cikin sauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta NECO a shafin hukumar na yanar gizo (results.neco.gov.ng) makonni kadan bayan jarrabawar.

Ana shawartar dalibai da su ziyarci shafin yanar gizon hukumar domin duba sakamakon jarabawarsu ta NECO da suka zana a shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Ya na murna ya tsere daga kurkuku, jami'an tsaro sun cafke shi

Yadda dalibai za su duba sakamakon jarabawar NECO 2024
An fitar da sakamakon NECO a kan shafin yanar gizon hukumar (results.neco.gov.ng). Hoto: Nony and sons
Asali: Facebook

Ana so daliban da za su duba sakamakonsu da su tanadi lambar rajistarsu ta NECO, lambar sirri da shekarar jarrabawarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta yi bayani daki daki na matakan da dalibai za su bi domin duba sakamakon NECO ta 2024 kamar yadda aka tanadar a shafin yanar gizon hukumar.

1. Ziyarci shafin NECO na yanar gizo

Matakin farko da dalibai za su dauka shi ne ziyartar shafin hukumar na yanar gizo. Ana so dalibai su ziyarci shafin NECO: www.neco.gov.ng domin duba sakamakon.

Dalibai a duk fadin kasar na iya ziyartar shafin ta wayar hannunsu ko na'ura mai kwakwalwa.

2. Sayen lambar duba sakamakon

Ana so dalibai su sayi wata lambar sirri ta musamman da za su yi amfani da ita wajen duba sakamakon NECO ta 2024.

Ana iya siyan katin a shafin NECO. Dalibai za su yi amfani da katin bankinsu ko kuma bayanan bankinsu wajen sayen lambobin.

Kara karanta wannan

'Ya ci mutuncin jam'iyya': PDP ta dakatar da tsohon dan takarar gwamna a Arewa

3. Shiga shafin duba jarabawar NECO

Ana sa ran dalibai za su ziyarci sashen duba sakamakon jarabawar a shafin yanar gizon NECO bayan sun sayi katin.

Za a bukaci dalibai su shiga shafin ta hanyar amfani da shekarar da suka zana jarabawa, nau'in jarabawa da kuma lambar sirrin da suka sayo.

4. Shigar da bayanan jarrabawar

Dalibai za su shigar da shekarar jarabawarsu (2024) da kuma nau'in jarabawar (June/July SSCE). Dalibai za su kuma shigar da lambobi 10 na jarawarsu ta NECO.

5. Duba sakamakon NECO

Dalibai za su danna maɓallin "Duba Sakamakon" domin duba sakamakon jarabawarsu ta NECO.

Za a nuna sakamakon nan take, dalibai za su ga makin da suka samu a kowane darasi. Ana so dalibai su fitar da sakamakon ko kuma ya adanashi a PDF domin amfanin gaba.

Jihohin da suka fi cin NECO

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zana jarabawar NECO ta ce kashi 60 na daliban da suka zana jarabawar a 2023 suka samu kiredit biyar da suka haɗa da Lissafi da Ingilishi.

Hukumar ta kuma bayyana cewa jihar Abia ce ta fi yawan ɗalibai da suka samu kiredit biyar ko sama da haka, inda Adamawa ta zo ta biyu da kuma Kebbi ta uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.