Hukumar shirya jarabawar NECO ta fallasa jahohin dake kan gaba wajen satar amsa

Hukumar shirya jarabawar NECO ta fallasa jahohin dake kan gaba wajen satar amsa

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandari ta Najeriya, NECO ta sanar da sakin sakamakon jarabawar da aka zana a watan Nuwamba da Disamba, inda ta ce jahar Ogun ce kan gaba wajen samun nasara a tsakanin kafatanin jahohin Najeriya.

Hukumar ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Feburairu ta bakin mukaddashin shugabanta, Abubakar Muhammed Gana, wanda ya bayyana cewa daliban jahar Ogun sun samu nasara da kashi 91.42.

KU KARANTA: Hukumar INEC za ta kirkiro sabbin rumfunan zabe kafin zaben gama gari na 2023

Daily Trust ta ruwaito Muhammad Gana yana cewa jaha ta biyu wajen samun nasara ita ce Akwa Ibom, inda dalibanta suka samu nasara da kashi 87.97, yayin da abin kunya, jahar Arewa, jahar Zamfara ta zo ta karshe da kashi 12.90, duk kuwa da cewa dalibai 230 ne kacal suka zana jarabawar.

Game da satar amsa dsa magudin jarabawa kuwa, hukumar shirya jarabawa ta NECO ta sanar da jahar Filato a matsayin jagora a tsakanin jahohin Najeriya wajen satar amsa inda aka samu matsalolin satar amsa da magudin jarabawa har kashi 21.31, yayin da jahar Oyo ke biye da ita da kashi 19.97.

Mohammed Gana yace duk da cewa an samu raguwar satar amsa a jarabawar na bara da kashi 5.9 idan aka kwatanta da jarabawar shekarar 2016, amma dai hukumar ta damu matuka da yadda har yanzu ake satar amsa a jarabawar, kuma za ta cigaba da iya kokarinta don magance matsalar.

Gana ya ce daga cikin dalibai 42,985 da suka yi rajistan jarabawar, 42,429 ne suka zana ta, yayin da 556 suka yi biris da ita, sai dalibai 24,098 suka samu maki mai darajan ‘C’ a darussa 5 da suka hada da Turanci da Lissafi.

Dalibai 32,917 kuma sun samu maki mai daraja ‘C’ a darussa 5 ba tare da la’akari da lissafi da turanci ba, adadin wadannan dalibai ya kai kashi 77.58. wannan ne karo na farko da NECO ta fitar da sakamakon jarabawa bayan kwanaki 38 da zana jarabawar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel