Gwamna Dauda Ya Fadi Lokacin Gamawa da Turji, Ya Tona Abin da Ke Rura Wutar

Gwamna Dauda Ya Fadi Lokacin Gamawa da Turji, Ya Tona Abin da Ke Rura Wutar

  • Gwamna Dauda Lawal Dare na Zamfara ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci a jihar baki daya nan kusa
  • Dauda Lawal ya ce yana da tabbacin an kusa kawo karshen kasurgumin dan ta'addan nan, Bello Turji da sauransu
  • Gwamnan ya dangantaka ta'addanci da ke faruwa a jihar da harkar hakar ma'adinai wanda ba za a raba su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sha alwashin kawo karshen rashin tsaro da ya addabi al'umma.

Gwamna Dauda Lawal Dare ya ce kwanakin kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji sun kusa zuwa karshe.

Gwamnatin Zamfara ta yi magana kan kawo karshen Bello Turji
Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya sha alwashin hallaka Bello Turji nan ba da jimawa ba. Hoto: Dauda Lawal.
Asali: Twitter

Dauda Lawal ya sha alwashin gamawa da Turji

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi halin da Turji da yan bindiga ke ciki bayan kisan Halilu Buzu

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a jiya Litinin 16 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauda Lawal ya ce nan ba da jimawa ba za a hallaka Bello Turji ko kuma a cafke shi domin kawo zaman lafiya.

Ya ce akwai alaka mai kyau da hadin guiwa tsakanin gwamnatin jihar da ta Tarayya a yaki da ta'addanci.

"Saboda hadin guiwa da muke da Gwamnatin Tarayya na tabbata nan ba da jimawa ba karshen Bello Turji zai zo."

- Dauda Lawal

Gwamna Dauda ya yabawa rundunar sojoji

Duk da ya ke gwamnan bai tabbatar cewa hallaka Turji zai kawo karshen ta'addanci ba amma ya ce hakan babbar nasara ce.

Ya tabbatar da cewa rundunar sojoji suna kan turba mai kyau wanda bai kamata su kauce daga kan haka ba.

Kara karanta wannan

"Mu na kokarinmu:" Gwamnan Katsina ya mika bukatu ga rundunar sojan sama

"Abin da ya kamata shi ne cigaba da kai hari da sojoji ke yi, idan muka dore a kan haka, nan da makwanni biyu zuwa wata daya labarin ta'addanci zai sauya."
"Akwai alaka mai karfi tsakanin ta'addanci da kuma hakar ma'adinai da ake yi wanda ba za ka raba su ba."

- Dauda Lawal

Dauda Lawal ya magantu kan ta'addanci

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta yi magana game da halin da ake ciki musamman bayan kisan Halilu Sabubu.

Gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare ya ce ya fi kowa farin ciki game da halin da ake ciki yanzu kan ayyukan ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.