Jerin Rikakkun Yan Ta'adda 7 da Gwamnatin Tinubu Ta Yi Nasarar Hallakawa
A ranar Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024 aka hallaka rikakken dan bindiga, Halilu Sabubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kisan dan ta'addan ya sanya farin ciki a zukatan yan Najeriya saboda yadda ya jefa al'umma a halin kunci saboda matsalar tsaro.
Gwamnatin Bola Tinubu ta yi nasarar hallaka kasurguman yan bindiga da dama wanda suka addabi al'umma musamman a Arewa maso Yamma.
Legit Hausa ta jero muku wadanda aka yi nasarar hallaka su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Baleri Fakai
Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun yi ajalin Baleri Fakai a yau Litinin 16 ga watan Satumbar 2024.
Baleri ya kasance na hannun daman rikakken dan bindiga, Bello Turji da ya addabi al'umma, kamar yadda Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na X.
2. Halilu Sabubu
Jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka dan ta'adda, Halilu Sabubu a ranar Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024.
An ayyana Sabubu wanda ake nema ruwa a jallo a watan Mayun 2024 da ta gabata.
3. Ali Kachalla
A ranar 12 ga watan Disambar 2023 aka hallaka Kachalla a karamar hukumar Munya da ke jihar Niger.
4. Dangote
Kasurgumin dan ta'adda, Dangote ya rasa ransa a watan Afrilun 2024 a jihar Katsina.
Dangote ya mutu yayin arangama da tsagin dan ta'adda, Dankarami a dajin karamar hukumar Batsari zuwa Jibia.
5. Damina
A watan Maris na 2024 jami'an sojoji suka yi nasarar hallaka Damina da ya addabi yankin Arewa maso Gabas.
6. Modi-Modi
Jami'an tsaro sun samu galaba inda suka hallaka dan ta'adda, Usman Modi-Modi a jihar Katsina.
Rahotanni sun ce an hallaka yan bindiga a fadan da suka hada da Mankare da Gunki Ummadau da Dogo Jabi da Harisu Babba a karamar hukumar Safana.
7. Yellow Jambros
A karshen shekarar 2023 aka hallaka kasurgumin dan ta'adda, Yellow Jambros a jihar Kaduna.
Sojojin saman Najeriya ne suka hallaka Jambros a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna.
Bulama ya kafa asusun tallafawa sojoji
Kin ji cewa Lauya Bulama Bukarti ya kaddamar da asusun tallafawa sojoji da suka hallaka Halilu Sabubu a jihar Zamfara.
Bulama ya ce a ƙungiyarsu sun tallafa da kudi har N1.8m domin karfafawa sojojin guiwa tare da nuna musu goyon baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng